✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Najeriya da gwamnatin sojin Nijar sun sasanta

Ministan Harkokin Wajen Nijar, Bakary Yaou Sangare da takwaransa na Najeriya Yusuf Tuggar sun tabbatar da cewa ƙasashen biyu sun shirya

Gwmanatin Sojin Nijar ta sanar da cewa sun sasanta da gwamnatin Najeriya, bayan watanni 20 ƙasashen suna zaman doya da manja.

Hakan ta faru ne bayan ziyarar aiki da Ministan Harkokin Wajen Najeriya, Yusuf Tuggar ya kai birnin Yamai, fadar gwamnatin Nijar.

Bayan sanya hannu kan takardar, Ministan Harkokin Wajen Nijar, Bakary Yaou Sangare, ya bayyana cewa, “da ma Najeriya ’yan uwanmu ne, duk wanda ya ce zai raba  Nijar da Najeriya, shi da kansa ya san ba gaskiya ba ne, abu ne na Allah. Allah Ne Ya haɗa wannan zumunta ka, babu wanda ya isa ya raba ta.”

Takwaransa na Najeriya, Yusuf Tuggar, ya bayyana cewa nan gaba Shugaba Bola Ahmed Tinubu za su gana da shugaban gwamnatin sojin Nijar, Janar Abdurrahman Tchiani, a matsayin ci gaban wannan daidaitawa.

Ya bayyana cewa yarjejeniyar da ƙasashen biyu suka sanya hannu a kai, ta zama, “darasi ga duk wasu ƙasashen duniya, domin yanzu an shiga wani lokaci da ake fama da tashe tashen hankali. To yanzu mu abin da a muka a tsakaninmu ya zama abin koyi.”

Abin da yarjejeniyar ta kunsa

Tuggar ya bayyana cewa yarjejeniyar da ƙasashen suka ƙulla ta danganci yin aiki tare domin tunkarar duk matsalolinsu a fannin, tsare, makamashi da sauran bangarori na tattalin arziki.

Sauran sun haɗa da kafa ofishin haɗin gwiwa na dindindin, sannan “a ƙara raya shi ya koma irin abubuwan da yake yi a da. Ta yadda gwamnoni da sauran shugabanni daga ɓangarorin biyu za su riƙa tattaunawa.”