✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutanen da suka saba ba ni abinci yanzu na neman taimako — Obi

Obi ya ce zai ci gaba da magana matuƙar abubuwa ba sa tafiya daidai a Najeriya.

Ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023, Peter Obi, ya ce talauci a Najeriya ya tsananta matuƙa har ta kai mutanen da suka saba ba shi abinci a baya yanzu suna neman taimako daga wajensa.

Obi, ya bayyana hakan ne a lokacin taron kwamitin zartarwa na ƙasa na jam’iyyar LP da aka gudanar a otal ɗin Transcorp Hilton da ke Abuja a ranar Laraba.

“Najeriya na rushewa. Lamarin tattalin arziƙi na ƙara taɓarɓarewa, mutane na ƙara shiga cikin talauci kullum,” in ji Obi.

“Ya kamata mu riƙa magana idan abubuwa ba sa tafiya daidai. Ka da mu ji tsoro. Waɗanda suka ji tsoro a baya, ba su yi wani abu mai amfani ba.”

Ya ce jam’iyyarsu tana shirya shiga babban zaɓen mai zuwa, inda za su fito da ‘yan takara masu nagarta da ƙwarewa daga matakin Majalisar Wakilai, Sanatoci, Gwamnoni har zuwa Shugaban Ƙasa.

Obi, ya kuma ƙaryata jita-jitar cewa yana shirin barin jam’iyyar LP tare da komawa wata jam’iyyar.

Ya ce bai tattauna da kowa ko wani ƙungiya kan ficewarsa daga jam’iyyar ba, kuma duk wani abu da za a yanke game da makomar jam’iyyar, za a yi ne tare da sauran mambobinta.

“Ban taɓa cewa zan bar jam’iyyar LP ba,” in ji shi.