Sanata Yemi Adaramodu, mai magana da yawun Majalisar Dattawa, ya ce matsalar tsaro a Najeriya na raguwa, kuma tattalin arziƙi ya fara farfaɗowa.
Ya yaba da ƙoƙarin da sojoji ke yi wajen yaƙi da ’yan bindiga da ’yan ta’adda.
- Haɗakar ’yan hamayya alheri ce ga siyasar Nijeriya — Gbajabiamila
- WFP ya dakatar da tallafin abinci a Yammaci da Tsakiyar Afirka
“Sojoji suna ƙoƙari saboda muna ba su isasshen kuɗi don siyan makamai da kula da jin daɗinsu. Yanzu matsalar ’yan bindiga ta ragu a wasu jihohi, kuma ana magance ta.”
Ya ƙara da cewa satar mutane ta ragu: “A da, mutane ba sa iya bacci saboda tsoro. Amma yanzu abubuwa sun ɗan gyaru. Sai dai waɗanda za su sa siyasa ne ba su yadda da hakan ba.”
A ɓangaren tattalin arziƙi kuwa, Adaramodu ya ce ana samun ci gaba kamar ƙarin fita da kayayyaki sama da shigowa da su kamar yadda aka saba a baya.
“A karon farko cikin shekaru, muna fitar da kaya sama da abin da muke shigowa da su. Yanzu muna fitar da gangar ɗanyen mai miliyan biyu a rana.”
Ya kuma bayyana cewa an biya wasu manyan basuka da ake bin Najeriya.
“IMF sun tabbatar min biya bashin da ya kai kimanin Naira tiriliyan huɗu. Yanzu mun kashe kashi 63 kacal don biyan bashi, ba 97 kamar yadda aka saba ba.”
Sai dai ya amince cewa mutane ba su fara ganin sauyin tattalin arziƙi ba tukunna.
“Kamar marar lafiya ne da aka fara yi masa magani sai an ɗan jima kafin ya warke. Haka ma tattalin arziƙinmu ke buƙatar lokaci.”
Ya ce yanzu gwamnatin ba ta ciwo bashi sai don yin ayyuka masu muhimmanci.
“Majalisa ba za ta amince da bashi ba sai an bayyana ainihin abin da za a yi da shi, kamar tituna ko ayyukan jin-kai.”
Adaramodu, ya buƙaci ’yan Najeriya da su ƙara hakuri kafin su fara sharɓar romon tattalin arziƙi.
“Tattalin arziki yana farfaɗowa. Ba da daɗewa ba mutane za su fara ganin sauyi.”