An gano gawar yara bakwai a yankin Mokwa, da ke Jihar Neja, bayan ambaliyar ruwa da ta afka wa garin mako guda da ya wuce.
Yawan adadin waɗanda suka rasu kawo yanzu ya kai mutum 160, amma wasu jami’ai sun ce za a iya gano gawar sama da mutum 200.
- Kotu ta aike da ɗan Tiktok gidan yari kan yin shigar mata a Kano
- Sallah: Mun shirya samar da tsaro a Yobe — ’Yan Sanda
Ambaliyar ta kuma tafi da motar haya mai kujeru 18 ɗauke da fasinjoji.
Kawo yanzu, bayan kwana shida da faruwar ambaliyar, ba a ga motar ko wani daga cikin fasinjojin ba.
Wani mazaunin garin, Baba Abu, ya ce: “Direban bai nemi ƙetare ruwan ba. Ya tsaya gefe yana jira ruwa ya ragu.
“Amma sai ruwan ya ƙaru ya kwashe motar ya jefa ta cikin Kogin Neja. Har yanzu ba mu san inda ta ke ba.”
Wasu daga cikin waɗanda ambaliyar ta shafa sun koka cewa ba sa samun kayan tallafi, duk da cewa gwamnati ta ce tana rabawa.
Hadiza Saidu, wadda ta rasa mahaifiyarta da komai nata, ta ce: “Da kayan jikina guda ɗaha da hijabi na tsira da su. Idan muka je karɓar tallafi, sai a ce ya ƙare. Wasu da ambaliyar ba ta shafa ba ake bai wa tallafin.”
Mutane sun fusata bayan wasu manyan cirarun jami’an gwamnati ne kawai suka ziyarci Minna, ba tare da sun je Mokwa inda ambaliyar ta faru ba.
Ƙungiyoyi da mazauna yankin sun ce hakan bai nuna an tausaya waɗanda lamarin ya shafa ba.
Gwamnati ta ce ambaliyar ta samo asali ne daga ruwan sama mai ƙarfi da kuma lalatacciyar hanyar ruwa, ba daga buɗe dam ba.
Masana da Ƙungiyar Tsofaffin Arewa (NEF), sun buƙaci gwamnati ta ɗauki matakan gaggawa don taimaka wa waɗanda lamarin ya shafa da kuma kare sake faruwar hakan a gaba.