Wasu kungiyoyin fararen hula guda 20 daga Arewacin Najeriya sun caccaki masu sukar tsare-tsaren tattalin arziki daga Gwamnatin Shugaba Tinubu ta bullo da su.
Kungiyoyin, karkashin jagorancin kungiyar Arewa Think Tank, sun soki masu adawa da shirin gwamnatin na dauke Hukumar Filayen Jiragen Sama (FAAN) da kuma wasu muhimman bangarorin Babban Bankin Najeriya (CBN) daga Abuja zuwa Legas.
“Karya ce ake yadawa ba cewa za a dauke hukumar FAAN da wasu rasssan CBN ne da nufin nuna wariyar siyasa ga wani yanki.
“Wannan shaci-fadi ne kawai, domin kuwa, an yi haka ne domin inganta ayyukan da hakan ya shafa da kuma rage kudin da ake kashewa wajen gudanar da su,” in ji kungiyoyin.
- Ali Nuhu ya kai wa Sarkin Kano ziyarar ban-girma
- NAJERIYA A YAU: Yadda Cin Ƙwai Ke Neman Gagaran ’Yan Najeriya
Sun bayyana haka ne a wata sanarwar bayan taron kwana biyu da suka gudanar, wanda Shugaban Kungiyar Arewa Think Tank, Muhammad Alhaji Yakubu, da wakilinn takwarorinsa 19, Injini Daniel Maikudi suka sa wa hannu.
A karshe sun bukaci Shugaba Tinubu ya kira taron kasa don tattauna wasu tanade-tanaden kundin tsari mulkin Najeriya tun daga samun mulkin kai zuwa yanzu, a mika su ga majalisar dokokin kasa domin yin gyaran fuska ga kundin tsarin mulki.
Kungiyoyin da suka halarci taron sun hada da kungiyar zaman lafiyar Arewa (NNP), Majalisar Matasan Arewa (AYA), Kungiyar Kare Rajin Arewa (ASP), Kungiyar Arewa ta Tsakiya (MBSG) da dai sauransu.
Sauran sun haka da kungiyar Gombe Front (GF), Kungiyar Cigaban Borno (BDA), Kungiyar Masu Kishin Kogi (KPY), Kugiyar tattaunawa ta Kaduna (KDG), Zauren Katsina (KF), da dai sauransu.