✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda kisan ’yan Arewa 16 a Edo ya tayar da ƙura a faɗin Nijeriya

Amnesty International ta ce mutane 16 da aka kashe ’yan asalin Jihar Kano ne.

Kisan wasu matafiya ’yan Arewa da aka yi a garin Uromi da ke Ƙaramar Hukumar Arewa maso Gabashin Esan ya tayar da ƙura a faɗin Nijeriya.

A bayan nan ne wasu hotunan bidiyo da aka yaɗa a shafukan sada zumunta suka nuna wasu mutane ɗauke da makamai suna far wa matafiyan da suka taso daga Kudanci zuwa Arewacin Nijeriya.

Hotunan bidiyon sun nuna yadda aka yi wa waɗanda abin ya shafa jina-jina sannan aka cinna musu wuta suka ƙone ƙurmus.

Tuni dai gwamnatin Edo ta yi Allah wadai da lamarin wanda ya faru a ranar Alhamis tare da ba da umarnin ƙaddamar da bincike a kai.

Wata sanarwa da Sakataren Labarai na Fadar Gwamnatin Edo, Fred Itua ya fitar, ta tabbatar da cewa ’yan sa- kai ne suka kai harin

Sanarwar ta ambato Gwamna Monday Okpebholoce na shan alwashin hukunta “masu laifin.”

“Binciken farko-farko ya nuna cewa matafiya ne da suka taso daga Fatakwal na Jihar Ribas suka ratso ta garin, sai ’yan banga suka kama su da tunanin cewa ɓatagri ne,” kamar yadda Fred Itua ya bayyana.

Sai dai sanarwar ba ta bayyana adadin mutanen da aka kashe ba a harin, amma ta ce Gwamna Okpebholo ya ziyarci garin a ranar Juma’a, inda ya yi alƙawarin gano waɗanda suke da hannu domin su fuskanci hukunci.

Yayin ziyarar da ya kai wurin da lamarin ya faru, Gwamna Okpebholo ya yaba wa shugabannin ’yan arewacin Nijeriya “bisa yadda suka kwantar da al’amarin cikin hikima” in ji sanarwar.

Mutum 16 aka kashe ’yan asalin Jihar Kano — Amnesty

Ƙungiyar kare haƙƙi ta Amnesty International ta ce mutane 16 aka kashe kuma ’yan asalin Jihar Kano ne.

“’Yan sa-kai sun tare matafiyan, suka fito da su daga motarsu, suka yi musu duka, sannan suka cinna musu wuta,” a cewar wani saƙo da Amnesty ta wallafa a shafukan sada zumunta.

Ta ƙara da cewa matafiyan na kan hanyar komawa garinsu na asali ne “domin yin bukukuwan sallah tare da iyalansu.”

Amnesty ta yi kira da a gaggauta gudanar da bincike kan lamarin tare da tabbatar anhukunta masu hannu a cikinsa.

Kwankwaso ya fusata

Jagoran jam’iyyar adawa ta NNPP kuma tsohon Gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi tir da kisan, inda ya nemi a gudanar da bincike.

Cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Kwankwaso ya bayyana harin a matsayin “rashin adalci”

Ya jaddada cewa duk wani ɗan Nijeriya na da ‘yancin yin tafiya a ƙasar nan ba tare da fargabar cin zarafi ko tsangwama ba.

“Abin da kowa ya sani shi ne, ya zama wajibi a bar ‘yan kasa su yi tafiya a duk faɗin kasar nan ba tare da fuskantar wata barazana ko cin zarafi ba.

“Ina kira ga hukumomin da abin ya shafa da su gudanar da cikakken bincike a kan wannan lamari mai tayar da hankali tare da tabbatar da an hukunta masu hannu a ciki,” in ji Kwankwaso.

Atiku ya bayyana kaɗuwarsa

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar ya bayyana kaɗuwarsa tare kiran mahukunta da su gaggauta ɗaukar matakan da suka dace kan lamarin

A saƙon da ya wallafa a shafinsa na X, Atiku ya ce “ina matuƙar baƙin ciki da rahotannin kisan gillar da aka yi wa wasu mafarauta a Jihar Edo.

“Ina miƙa ta’aziyyata ga iyalai da ’yan uwan waɗanda abin ya shafa.

“Wannan mummunan lamari yana buƙatar cikakken bincike domin ganowa da kuma tabbatar da cewa an gurfanar da waɗanda ke da hannu a ciki.”

Atiku ya kara da cewa “kare rayukan waɗanda da ba su ji ba ba su gani ba dole ne ya kasance abu mai muhimmanci.

“Kuma ina kira ga hukumomi da su gaggauta ɗaukar mataki don hana sake afkuwar wannan lamari na ɗaukar doka a hannu.”

A tabbatar an kamo masu hannu a aika-aikar — Tinubu

Shi ma Shugaba Bola Tinubu ya yi Allah-wadai da kisan yana mai umartar hukumomin tsaro da su kamo waɗanda suka yi wannan mummunar aika-aikar.

“Ba za a bari miyagu su ci gaba da zubar da jinin ‘yan Nijeriya ba tare da hukunta su ba.

“Dole ne a yi adalci,” a cewar wata sanarwa da mai magana da yawun Shugaban Ƙasa, Bayo Onanuga ya fitar.

Ba za mu yarda ba — Gwamnonin Arewa

Ita ma ƙungiyar gwamnonin Arewa (NSGF) ta ce ba ta yarda da wannan lamari ba wanda kuma ta yi Allah-wadai da shi.

A wata sanarwa da shugaban kungiyar kuma gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya fitar a ranar Juma’a, ya bayyana harin a matsayin ƙololuwar take haƙƙin bil’adama.

Ya jaddada cewa, cin zarafi ba abu ne da ba za a amince da shi ba, “kuma dole ne mu yi Allah wadai da shi.”