✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jirgin soji ya kashe ’yan sa-kai 20 da ke fatattakar ’yan bindiga a Zamfara

Jiragen sojin sun kashe wasu ’yan sa-kai bisa kuskure, a yayin da ’yan sa-kan suke ƙoƙarin fatattakar ’yan bindiga da suka kai hari a yankin…

Aƙalla mutane 20 ne suka mutu bayan wani hari da jiragen sama na sojojin Najeriya (NAF) ya kai domin fatattakar ’yan bindiga a a Jihar Zamfara.

Jiragen sojin sun kashe wasu ’yan sa-kai bisa kuskure, a yayin da ’yan sa-kan suke ƙoƙarin fatattakar ’yan bindiga da suka kai hari a yankin Mani a Ƙaramar Hukumar Maru.

Jiragen sojin sun kai hare-haren ne domin fatattakar ’yan bindiga da suka kai wa manoma hari a kan babura da rana tsaka.

Mazauna yankin sun ce bayan ’yan bindiga sun sace manoma sama da 50 ne jirgin sojin ya amsa kiran gaggawa, amma aka samu kuskure ya kashe wasu ’yan sa-kai da ke ƙoƙarin fatattakar maharan.

Wani mazaunin yankin ya shaida wa kafar BBC cewa, “Mun sanar da jami’an tsaro bayan harin, amma kawai sai muka ga jirgin ya zo ya kashe ’yan sa-kai na mu.”

Wani mazaunin garin ya ce, a yayin da jama’a ke ƙoƙarin taimaka wa wadanda aka kai wa hari, sai ga wani jirgin saman soji ya iso.

Ya ce, “’Yan bindigar sun tafi da mutane 50, amma yayin da muke ƙoƙarin kai ɗauki, sai muka ga jirgin soji, kuma ya fara harbin mu. Kowa ya gudu neman mafaka,” inda ya ƙara da cewa sun yi kamar matattu ne don su tsira.

Wani mazaunin kuma ya yi kira ga jami’an tsaro da su ƙara yawa, inda ya buƙaci a yankin amma su yi taka-tsantsan yayin gudanar da ayyukan.

Har yanzu sojojin Najeriya ba su ce komai ba game da lamarin.

Idan ba a manta ba, ire-iren wannan harin huskure ya faru a baya a yankin Jihar Zamfara. A watan Janairun 2025, wani harin jirgin saman sojin Najeriya ya kashe mutane 16 bisa kuskure, ciki har da ’yan sa-kai da manoma, a ƙauyen Tungar Kara a Jihar Zamfara, bayan an zaci su ’yan bindiga ne.

Hakazalika, a watan Disambar 2024, wani harin jirgin sama a Jihar Sakkwato ya kashe fararen hula 10 a sakamakon abin da Gwamnan jihar ya bayyana a matsayin harin kuskure kan fararen hula.

A watan Disamban shekarar 2023 wani jirgin soja ya kai irin harin inda ya kashe sama da fararen hula kimanin 100 a wurin taron Mauludi a yankin Tudun Biri da ke Ƙaramar Hukumar Igabi a Jihar Kaduna.