✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Harin ’yan bindiga ya sa Zamfarawa sun koma kwana a jeji

Daga cikin waɗanda aka yi garkuwa da su har da wani magidanci da matansa biyu da ’ya’yansa uku a yankin Ƙaramar Hukumar Kaura Namoda

Mutane sun koma kwana a cikin jejin a sakamakon hare-haren ’yan bindiga a yankin Ƙaramar Hukumar Ƙaura Namoda da ke Jihar Zamfara.

Mazauna yankunan sukan dawo cikin gari su yini, idan dare ya yi kuma su shiga daji su kwana, sakamakon ƙaruwar hare-haren ’yan ta’adda, inda suka kashe mutum huɗu suka yi garkuwa da wasu 26.

Wani mazaunin Ƙauran Namoda da ya buƙaci a ɓoye sunansa ya ce adadin mutanen zai iya cin haka, inda ya tabbatar cewa maharan sun kashe wata mata tare da sace wasu 26.

Ya bayyana cewa daga cikin waɗanda aka yi garkuwa da su har da wani magidanci da matansa biyu da ’ya’yansa uku.

Wani ganau ya ce lamarin ya fi muni a ƙauyen Sabon Gari inda ’yan bindiga suka kashe wata mata sannan kuma yi garkuwa da wasu mutane sama da 20.

’Yan ta’addan sun tsananta kai hare-hare a kan ƙauyuka inda a Asabar da misalin karfe 1:30 suka kai hare-haren, duk kuwa da cewa an girke jami’an tsaro a garin Ƙaura Namoda.

Wata majiya a yankin ta ce ana zargin ’yan ta’addan suna da alaƙa da jagoran ’yan bindiga, Bello Ƙaura, wanda aka fi sani da Ɗan Sade, wanda ya ya addabi ƙananan hukumomin Ƙaura Namoda da Bunguɗu da kuma Maradun.