Aƙalla mutum uku aka kashe, yayin da aka sace 26 a wani sabon harin da ’yan bindiga suka kai yankin Ƙaramar Hukumar Kaura Namoda, a Jihar Zamfara.
Harin ya faru ne daga ranar Alhamis zuwa Asabar a ƙauyukan da suka haɗa da Sabon Gari da Kungurki.
- Mataimakiyar shugaban majalisar dokokin Edo ta yi murabus
- Hajji: Gwamnan Gombe ya yi bankwana da maniyyata 966, ya bai wa kowa kyautar Riyal 200
Wani mazaunin yankin ya ce: “Mutane sun fara barin gidajensu da daddare, suna dawowa ne da safe. Hare-haren da ake kai wa Sabon Gari da maƙwabtan ƙauyuka na ƙara tsananta.”
Ana zargin yaran wani ƙasurgumin ɗan bindiga mai suna Bello Kaura wanda aka fi sani da Dan Sade ne da kai wannan harin.
Wata majiya ta ce yana da sansani kusa da Sabon Gari.
Wani mazaunin ya ƙara da cewa: “Muna roƙon gwamnati ta kafa sansanin soja a Kungurki.
“Waɗannan ’yan bindiga na kai mana hari duk lokacin da suka ga dama, rayuwarmu tana cikin firgici.”
A wani harin da suka kai, mutum huɗu suka kashe, tare da sace wani mutum ɗaya.
Daga baya, ’yan bindigar sun nemi a biya su Naira miliyan uku a matsayin kuɗin fansa amma suka ƙi barin kowa ya ji muryar wanda suka sace.
Gwamna Dauda Lawal ya tabbatar da ƙarin goyon bayansa ga hukumomin tsaro tare da ƙaddamar da dakarun sa-kai na Community Protection Guard domin taimakawa wajen kare al’umma.