Shugaban Riƙo na Jihar Ribas, Ibok Ibas, ya ce Shugaba Bola Tinubu, ya naɗa shi ne domin dawo da zaman lafiya a jihar, wadda ke fama da rikicin siyasa.
Da yake jawabi a wani shirin talabijin a daren Alhamis a Fatakwal, Ibas ya bayyana naɗin nasa a matsayin matakin da ya dace don kawo ƙarshen rikicin siyasa da ya ɗauki kusan shekaru biyu.
- Farashin fetur na iya tashi bayan Dangote ya daina sayar da mai a Naira
- Muhimman ayyuka 8 a goman ƙarshe na Ramadan
Ya ce rikicin ya hana ci gaban gwamnati, tare da haifar da matsalar tsaro da koma bayan tattalin arziƙi a jihar.
“A matsayina na ɗan yankin Neja Delta, na fahimci damuwar mutanenmu. Rashin tabbas a Jihar Ribas ya shafi iyalai, ’yan kasuwa da rayuwar yau da kullum.
“Naɗin da aka yi min ba na siyasa ba ne, sai dai don dawo da doka da oda, tare da tabbatar da cewa mutanenmu suna rayuwa cikin kwanciyar hankali.”
Ya tabbatar wa al’ummar jihar cewa babban aikinsa shi ne dawo da zaman lafiya, tabbatar da bin doka da oda, tare da samar da yanayin da zai ba da damar ci gaban gwamnati da bunƙasa tattalin arziƙi.
“Ba aikin mutum ɗaya ba ne. Dole ne al’ummar Ribas su haɗa kai, dattawa, sarakunan gargajiya, ’yan siyasa, ’yan kasuwa, matasa da ƙungiyoyin fararen hula.
“Na zo a matsayin wanda zai hidimta wa jihar, wanda ke da nauyin dawo da zaman lafiya da tsari, domin Jihar Ribas ta dawo da matsayinta na cibiyar arziƙin man fetur a Najeriya.”
Ibas, ya gargaɗi ’yan jihar da su guji tashin hankali da aikata laifuka, inda ya bayyana cewa gwamnati ba za ta yarda da duk wani yunƙuri na kawo ruɗani ba.
Sai dai ya tabbatar da cewa zai mutunta haƙƙoƙin ’yan ƙasa tare da bin doka.
Ya buƙaci jama’a da su haɗa kai don girmama juna da samar da zaman lafiya a jihar.