✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotun Koli ta sanya lokacin yanke hukunci kan Zaben Gwamnan Kano

Koun Koli ta kebe ranar da za ta yanke hukunci kan Shari'ar Zaben Gwawmnan Jihar Kano wanda Gwamna Abba Kabir ya daukaka zuwa gabanta.

Kotun Koli ta kebe ranar da za ta yanke hukunci kan Shari’ar Zaben Gwamnan Jihar Kano wanda Gwamna Abba Kabir ya daukaka zuwa gabanta.

A ranar Alhamis ne kwamitin alkalai biyar karkashin jagorancin Mai Shari’a Inyang Okoro ya ajiye ranar yanke hukunci bayan sauraron lauyoyin bangarorin da ke shari’a da juna.

Gwamna Abba da Jam’iyyarsa (NNPP) sun daukaka da karar ne suna kalubalantar hukuncin da Kotun Daukaka Kara da ya kwace kujerarsa.

NNPP kuma tana sanar da kotun koli kan sabanin da ke cikin rubutaccen hukuncin kotun duakaka karar da ya tabbatar da nasarar zaben gwamna tare cin tarar masu karar sa Naira miliyan daya.

Ana iya tuna cewa ranar 17 ga Nuwamba, kwamitin alkalai mai mutum uku karkashin jagorancin mai shari’a Moore A. Adumein ya bayyana Nasiru Yusuf Gawuna na Jam’iyyar APC a mayin wanda ya lashe zaben gwamnan Kano.

Alkalan sun bayyana cewa Abba Kabir Yusuf ba dan Jam’iyyar NNPP ba ne a lokacin da aka gudanar da zaben, saboda ba shi da rijista, don haka bai cancanci tsayawa takara ba.

Sai dai a zaman Kotun Kolin na ranar Alhamis, jam’iyyun sun yi doguwar muhawarar kan batutuwan da suka shafi hurumin kotun daukaka karar a kan matsayin dan takarar jam’iyyar siyasa.

Lauyoyin sun kuma yi muhawara kan ko kotun za ta iya waiwayar kuskuren INEC na rashin sanya hannu a kan takardun zabe sama da 160,000 a zaben Gwamnan Kanon da aka shari’ar a kai.