More Podcasts
Jam’iyyar NNPP wadda Dakta Boniface Aniebonam ya kafa a shekarar 2001, ta samu ƙarfi sosai a Jihar Kano bayan tsohon Gwamna Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya shiga cikinta a shekarar 2022 tare da mabiyansa na Kwankwasiyya.
Shigowarsa ta farfaɗo da jam’iyyar, inda ta samu gagarumar nasara a zaɓen 2023 ta hanyar lashe kujerar gwamna da wasu kujerun majalisa.
Sai dai rikicin cikin gida da na shugabanci sun dabaibaye jam’iyyar, wanda hakan ya haddasa ficewar wasu manyan ’ya’yanta zuwa APC, lamarin da ke haifar da tambaya kan makomar NNPP a Kano.
Shin NNPP za ta kai labari a Kano, musamman bayan ficewar wasu jiga-jiganta?
- NAJERIYA A YAU: Kuskuren JAMB Da Ya Haddasa Faduwar Ɗalibai A Jarabawa
- DAGA LARABA: Tasirin Mulkin Karɓa-Karɓa A Najeriya
Wannan shi ne batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi duba.
Domin sauke shirin, latsa nan