Kotun Daukaka Kara ta tabbatar wa Gwamnan Jihar Nasarawa, Abdullahi Sule na Jam’iyyar APC kujerarsa, ta soke hukuncin kotun korafin zabe da a baya ta soke zabensa.
Alkalan kotun su uku da suka sanar da hukuncin a ranar Alhamis sun yi ittifakin cewa kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar ta yi kuskure wajen soke nasarar Abdullahi Sule na APC a zaben Gwamnan Nasarawa da aka gudanar ranar 18 ga Maris, 2023.
A safiyar Alhamis ne suka soke hukuncin kotun farkon suka tabbatar da nasarar Abdullahi Sule, wanda ke wa’adinsa na biyu a matsayin gwaman jihar.
Kotun Daukaka Karar yanke hukuncin bayan Abdullahi Sule ya daukaka kara zuwa gabanta bay kanotun sauraron korafin zaben gwamann jihar, ta kwace kujerarsa ta ba wa babban abokin hamayyansa, David Ombugadu na jam’iyyar PDP.
Ombugadu ya garzaya kotu ne Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta bayyana Adullahhi Sule na Jam’iyyar APC a matsayin wanda ya yi nasara da kuri’u 347,209, Ombugadu na biyu kuma ya zo na biyu da kuri’u 283,016.
Amma a zaman kotun shari’ar zaben na ranar 2 ga Oktoba, ta soke zaben Abdullahi Sule tare da ayya Ombugadu a matsayin halastaccen zababben Gwamnan Jihar Nasarawa.
Amma Gwamma Abduullahi Sule, ta hannun lauyansa, Wole Olanipekun (SAN), ya daukaka kara yana nema Kotun Daukaka Kara ta Tarayya ta soke hukuncin farkon ta tabbatar da nasararsa.
A martanin lauyan PDP da Ombugani, Kanu Agabi, ya bukaci kotun daukaka karar ta kori bukatar Abdullahi Sule, domin kotun sauraron karar zaben ta rika ta yi duk abin da ya kamata wajen bin diddigin karar da suka shigar kuma ta tabbatar da nasarar Ombugadu.
Kotun daukaka kara dai a halin yanzu ta dawo wa Abdullahi Sule da kujerar.