Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Babachir Lawal, ya ce goyon bayan da wasu gwamnonin APC suka nuna wa Shugaba Bola Tinubu domin ya sake tsayawa takara a 2027 bai dame su ba.
Ya ce su a cikin ƙungiyarsu ta masu haɗaka sun fi mayar da hankali ne kan talakawa, ba shugabanni ba.
- Gwamnatin Gombe za ta taimaki ’yar shekara 14 da aka yi wa auren dole
- Ndume ya jinjina wa Tinubu kan bai wa ’yan Arewa sabbin muƙamai
“Ko da dukkanin gwamnonin jihohi 36 da Abuja sun koma APC, babu abin da zai canja.
“Su da danginsu ba su fi ƙuri’u 1000 ba. Abin da muke so shi ne jama’a,” in ji Lawal a hirarsa da jaridar Nigerian Tribune.
Ƙungiyar masu haɗaka ƙarƙashin jagorancin Atiku Abubakar, Peter Obi, da Nasir El-Rufai ta zaɓi jam’iyyar ADC a matsayin jam’iyyar da za su kara da APC a zaɓen 2027.
“Mun ƙudiri niyya sosai. Muna da ƙwarewa kuma muna aiki a hankali. A lokacin da ya dace ne za mu bayyana wa duniya shirinmu,” in ji shi.