✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

2027: ’Yan Najeriya sun yi watsi da takarar Tinubu, sun koka kan tsadar rayuwa

Wasu na ganin wannan goyon bayan ba komai ba ne face muradin ci gaba da riƙe madafun iko.

’Yan Najeriya daga kowane ɓangare daban-daban sun caccaki jam’iyyar APC bisa yanke shawarar goyon bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu a matsayin ɗan takararta na shugaban ƙasa a zaɓen 2027, duk da cewa shekararsa biyu kacal da hawa mulki.

Wasu na ganin matakin ya nuna rashin tausayi da rashin damuwa da halin ƙuncin da al’umma ke ciki.

Jagororin jam’iyyar APC, gwamnoninta da ’yan majalisa ne suka fito suka nuna goyon bayansu ga Tinubu.

Amma jama’a na ganin hakan na nuna burin ci gaba da riƙe madafun iko ne kawai, ba wai taimakon talakawa ba.

Ra’ayoyi daga sassa daban-daban na Najeriya

A Jihar Legas, Mary Okonkwo, wata ’yar kasuwa ta ce: “Rayuwa na neman gagarar jama’a. Kasuwancina na shirin durƙushewa saboda hauhawar farashi. Kuma suna maganar zaɓe tun yanzu?”

Daga Fatakwal, Daniel Etim, ma’aikacin gwamnati ya ce: “Wannan goyon bayan da suka yi ya yi wuri da yawa, kuma ya nuna rashin mutunta mutane. Albashi ko mako ɗaya ba ya ishar mu.”

A Enugu, ɗalibar jami’a Adaeze Nnaji tambaya ta yi: “Shin wannan ne ladan wahalar da muke sha? Babu wutar lantarki, babu aiki, amma ana yaba wa shugaba wanda bai yi komai ba?”

A Abuja, Rashida Muhammad ta ce: “Tinubu ya ci amanarmu. Komai ya yi tsada kuma muna cikin tsananin wahala. Bai cancanci wa’adi na biyu ba.”

Tafawa Muhammad, wani manomi a Kano ya ce: “Farashin abincin kifi da taki ya ninka sau uku. Aikin gona na ya kusa durƙushewa.”

A Ibadan, Dele Olatunji, malamin makaranta ya ce: “Wadannan goyon baya ba don al’umma ba ne. Sun fi damuwa da kansu.”

Masana siyasa na ganin wannan goyon baya bai dogara da aiki ba, sai dai neman ci gaba da mulki.

Farfesa Hassan Saliu, ya gargaɗi cewa Najeriya na dab da zama ƙasa mai jam’iyya ɗaya.

Ya shawarci al’umma da su zauna cikin shiri domin su ɗauki mataki a 2027.

Wani masanin, Dokta Kabiru Sufi, ya ce ’yan siyasa sun fi mayar da hankali kan zaɓe fiye da warware matsalolin da ke addabar ƙasa, kamar tsaro, talauci da yunwa.

Duk da wannan goyon baya da jam’iyyar APC ta nuna, yawancin ‘yan Najeriya na buƙatar shugabanci na gari ne, ba wai alƙawura marasa amfani ba.

A cewar Adaeze Nnaji: “A gyara ƙasa tukunna sai a zo a yi maganar zaɓen 2027.”