Gwamnan Jihar Akwa Ibom, Fasto Umo Eno, ya bayyana shirinsa na ficewa daga Jam’iyyar PDP zuwa APC, inda ya umarci duka Kwamishinoninsa da sauran masu riƙe da muƙaman siyasa da su sauya sheƙa tare da shi ko kuma su sauka daga muƙamansu.
Da yake bayani a Uyo babban birnin jihar ranar Alhamis, gwamnan ya ce ba zai yi aiki da waɗanda ya naɗa su, su yi aiki da wata jam’iyya ba.
- An kama yarinya kan kashe jariri a sansanin ’yan gudun hijira
- Sojoji sun kashe mayaƙan ISWAP 16 a Borno
Gwamna Eno ya bayyana cewa Jam’iyyar PDP ba ta da taswirar da za ta tabbatar masa da tafiyarsa cikin kwanciyar hankali a zaɓuka, yana mai cewa yana da yaƙinin cewa zai ci zabe a ƙarƙashin kowace jam’iyya saboda ya yi aiki tuƙuru.
Ya bayyana cewa, ya koma Jam’iyyar APC ne saboda ya yi imani da gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu, kuma ba zai iya ci gaba da zama a Jam’iyyar PDP da goyon bayan shugaban Ƙasa kamar yadda Nyesome Wike yake yi a halin yanzu.
Gwamna Eno ya ce duk da yana ƙaunar PDP, ba ya hango nasarar jam’iyyar a zaɓuka masu zuwa, sakamakon rigingimun da jam’iyyar ke ciki.
“Ina son PDP, kuma ina son zama a cikinta, amma a bayyane take ƙarara cewa babu wani ma’auni da zan iya auno wa kaina nasara a zaɓukan da ke tafe..,” in ji shi.