✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kano: Nasarar Abba a Kotun Daukaka Kara ba kuskuren rubutu ba ne —Farfesa Odinkalu

Farfesa a fannin shari'a Chidi Odinkalu, ya ce kundin shari'ar kotun daukaka kara da ke tabbatar da nasarar Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ba kuskuren…

Farfesa a fannin shari’a Chidi Odinkalu, ya ce kundin shari’ar kotun daukaka kara da ke tabbatar da nasarar Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ba kuskuren rubutu ba ne.

Da yake tsokaci kan takaddamar hukuncin kotun, Farfesa Odinaku, tsohon Shugaban Hukumar Kare Hakkin Dan Adam na Najeriya ya bayyawa wa gidan talabijin na Channels cewa, ko kadan ba za a kira abin da ke cikin kudin shari’ar kuskuren rubutun alkalan kotun ba.

“Wannan ba kuskuren rubutu ba ne. Wannan tsohon zance ne. Babu kotun da ta san abin da yake yi da za ta fitar da irin wannan hukunci har ta sanya hannu a kai.

“Sai dai watakil a kotun gargajiya, ba ma kotun yanki ba, ballantana babbar kotu.

“Kotu Daukaka Kara ita ce ta biyu a Najeriya, don haka duk lauyan da ya san aikinsa dole wannan ya ba shi mamaki.”

A ranar Juma’a kotun daukaka karar ta karanta hukuncinta da ke korar karar Gwamna Abba, ta ayyana Nasiru Yusuf Gawauna na APC a matsayin wanda ya lashe zaben Gwamnan Kano.

Hukuncin ya yi watsi da karar da Abba ya daukaka, ya kuma tabbatar da hukuncin kotun karbar korafin zaben gwaman jihar.

Sai dai kuma kundin hukuncin da kotun daukaka karar da ta fitar ya rushe hukunta da ma na kotun farko, tare da tabbatar da nasarar Abba — wanda ya haifar da rudani.

Kotun da lauyoyin APC dai sun bayyana cewa kuskuren rubutu ne aka samu, ta kuma bukaci bangarorin da ta mika wa kundin da su dawo da shi.

Amma NNPP da magoya bayanta sun yi watsi da bayanin nata, inda a ranar Laraba, magoya bayan jam’iyyar suka gudanar da zanga-zanga a Kano kan neman tabbatuwar kujerar Abba.