✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Harin Masallacin Kano ya bar marayu 100, mata 13 sun shiga takaba

Wata matar aure ta rasa danta da mijinta da dan uwanta a harin Masallacin Larabar Abasawa

Yara 100 ne suka zama marayu sakamakon wuta da aka cinna wa mahaihansu a lokacin da suke jam’in Sallar Asuba a cikin masallaci a Jihar Kano.

Kazalika matan aure 13 sun zama zawarawa a sakamakon wannan harin da wani matashi shekara 38 ya kai wa masallatan a kauyen na Labarar Abasawa da ke Karamar Hukumar Gezawa ta jihar.

Aminiya ta gano cewa kawo yanzu mutane 17 sun rasu cikin wadanda harin masallacin ya ritsa da su, inda a halin yanzu ake zaman makoki a unguwar Gidan Goro da ke kauyen.

Mijina, dana da dan uwana sun rasu —Matar aure

Wakikinmu a yi kicibus a Asibitin Kwararru na Murtala Muhammad da ke Kano, da wata dattijuwa wadda ta ce mijinta da danta da kuma mijinta sun rasu a ibtila’in Masallacin Larabar-Abasawa.

Dattijuwar ta ce, “Akalla wata guda ake zaman jimami a Larabar Abasawa saboda yadda wannan abin tashin hankali ya shafi gida je daban-daban.”

Wakilin namu ya kuma ga wani matashi da ya tsallake rijiya da baya a harin da kuma ba mai tsanani sosai ba, wandda yake jinya a asibitin na Murtala.

Matashin mai shekaru 25, mai suna Shuaibu Ibrahim ya samu ’yan uwansa mata sun fito da shi shan iska a wajen dakin, kowannensu na kimanin aika-aikan da aka yi musu a masallacin.

Yadda abin ya faru

Kimanin mutane 40 ne suke jam’in sallar Asuba a masallacin lokacin da wanda ake zargin, mai suna Shafi’u, ya shiga ciki ya sanya makamashi ya tayar da wuta sannan ya kulle masallacin ya tsere.

Majiyoyi a kauyen da ma hukumomin tsaro sun ce rikicin gado da ya ki ci ya ki cinyewa a dangin su matashin ne ya sa shi yin wannan danyen aiki.

A halin yanzu dai wanda ake zargin yana hannun rundunar ’yan sanda ta Jihar Kano, inda ya kai kansa bayan ya yi wannan aika-aika a ranar Laraba, 15 ga watan nan na Mayu, 2024.

Yawan wadanda suka rasu

Tun a ranar mutane takwas suka ce ga garinku nana, a yayin da aka kai wasu sama da 20 Asibitin Kwararru na Murtala Muhammad da ke Kano.

Binciken Aminiya ya gano cewa 23 daga cikinsu an kwantar da su ne a dakin tiyata na asibitin, wani mutum uda kuma an kai shi Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano inda likitoci suka sanar cewa ya rasu.

Yanzu kwana biyar, mutum 17 ne suka rasu a yayin da wasu bakwai suke kwance a asibiti rai a hannun Allah.

Wani jami’in lafiya a asibitin Murtala da ya nemi a boye sunansa ya ce majinyatan suna cikin halin rai-kwakwai-mutu-kwakwai, sai dai abin da Allah Ya yi.

Marayu da zawarawa

A ziyarar karshe da Aminiya ta kai kauyen, ta iske al’ummar cikin yanayi na juyayi.

Mazauna kauyen sun shaida mana cewa magidantan da suka rasu a masallacin sun bar yara 100 da matan aure 13.

Daya daga cikin shugabannin kauyen mai suna Musa Muhammad, wanda Makwabcin masallacin da abin ya faru ne yabce, “Kusan duk wadanda abin ya rutsa da su, wadanda suka rasu da wadanda suke kwance a asibiti zuri’ar gida guda ne.

“Hudu ne kawi daga cikinsu ba su da aure, sannan daga cikin mamatan akwai magidanci daya da ke da ’ya’ya 19, akwai kuma mai ’ya’ya 17

“’Yan gida ɗaya ne. Game da gado kuwa, mahaifin shi Shafi’un ai bai ci gadon mahaifinsa ba, saboda kakan yaron ya riga shi rasuwa.

“Game da ikirarin matashin na cewa auren dole za a yi masa, ba gaskiya ba ne, domin kuwa yarinyar da aka so ya aura din ta riga ta auri wani tun tuni kuma har yanzu tana gidan mijin nata da ’ya’yanta biyu.”

Zargin tabin kwakwalwa

Wani dan uwan wanda ake zargin mai suna Shehu Abubakar ya bayyana cewa Shafi’u mutum ne mara magana kuma ba ya son shiga cikin jama’a.

A cewarsa, suna zargin dan uwan nasu na da matsalar kwakwalwa, saboda an taba kai shi asibiti domin duba lafiyar kwakwalwar tasa.

“Ba za mu iya cewa ga matsalar ba, amma ba ya magana mai tsawo da mutane, ba ya shiga jama’a, ba shi da aboki, kuma shi ba mai magana ba ne.

“An taba kai shi asibiti aka duba lafiyar kwakwalwarsa,” in ji Ibrahim.

Tururuwar ta’aziyya

A yayin da jami’an tsaro ke ci gaba da tsare wanda ake zargin, manyan jami’an gwamnatin Kano, ciki har da mataimakin gwamna, Aminu Abdulsalam da da Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero dackian Sarkin Gaya, Alhaji Aliyu Ibrahim Abdulkadir, sun kai wa al’ummar Larabar Abasawa ziyarar ta’aziyya tare da bayyana kaduwarsu bisa abin da ya faru.

Sarkin Gaya ya kuma ba wa iyalan gudummawar Naira miliyan uku domin rage musu raɗaɗin.

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP, Peter Obi, na daga cikin wadanda suka ziyarci majinyatan a asibiti domin duniya da yi musu fatan samun sauki.

Peter Obi ya kuma mika ta’aziyyarsa ga al’ummar yankin da ma gwamnatin jihar.