✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Majalisar Kano za ta yi wa dokar masaratu gyaran fuska

An dai jima magoya bayan siyasar Kwankwasiyya suna neman a dawo da Sarkin Kano na 14, Muhammadu Sanusi II kan kujerar Sarkin Kano

Majalisar Dokokin Kano ta amince da bukatar yin gyaran fuska ga dokar masarautu da nadin sarakuna ta jihar.

Shugaban Masu Rinjayen majalisar kuma mai wakiltar Mazabar Dala, Hussien Dala, ne ya gabatar  da kuudrin a ranar Talata, ya kuma samu amincewan takwarorinsa.

An dai jima magoya bayan siyasar Kwankwasiyya suna kiraye-kirayen dawo da Sarkin Kano na 14, Muhammadu Sanusi II kan kujerarsa da gwamnatin jihar da ta gabata ta Abdullahi Ganduje ta sauke daga kujerar Sarkin Kano.

Masu kiraye-kirayen na kuma neman ganin an soke sabbin masaraut Bichi, Gaya, Rano da kuma Karaye da ta kirkiro.

A daya bangaren kuma akwai masu adawa da soke sabbin masarautun.

Wasu dai na fargabar gyaran fuska ga dokar masarautun zai kai ga soke sabbin masarautun da aka nada ko rage wa sarakunansu daraja.