✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama mutum 78 da makamai da kwayoyi a Kano

An kama sanannen dillalin miyagun kwayoyi, Sulaiman Danwawu, da wasu haramtattun kwayoyi an taba kama shi

An kama mutane 78 tare da kwace tulin miyagun kwayoyi da makamai da kayan sata a wani samame da ’yan sanda suka kai kwanan nan domin ayyukan laifi a Jihar Kano.

A yayin samamen, an kama gawurtaccen dillalin miyagun kwayoyi, Sulaiman Danwawu, da wasu haramtattun kwayoyi bayan an taba kama shi a shekarar 2022.

Daga cikin sauran wadanda aka kama har da wani da ake zargin dan fashi da makami ne da bindigogi biyu da harsasai.

Kwamishinan ’yan sanda, Ibrahim Adamu Bakori, ya sanar a taron ’yan jarida da ya gudana a hedikwatar rudunar da ke Bompai a ranar Juma’a cewa aikin kamen ya yi daidai da umarnin Shugaban ’Yan Sanda na Kasa kan a aiwatar da ingantattun matakai domin dakile ayyukan laifi.

Ya bayyana cewa hnyoyin da rundunarsa ta yi amfani da su sun hada da sintiri na sa’o’i 24, kai samame bisa bayanan sirri, da kuma hadin gwiwa da al’umma.

Tsakanin 23 ga Afrilu zuwa 9 ga Mayu, ’yan sanda sun kama mutane biyar bisa zargin fashi da makami, bakwai bisa zargin sayar da miyagun kwayoyi, da wasu bisa zargin satar shanu, damfara, sata, da kuma ‘yan daba.

Kayayyakin da aka kwato sun hada da bindigogi, miyagun kwayoyi, motoci, babura mai kafa uku, babura, muggan makamai, kudin jabu, dabbobi, da kayan lantarki.

Kwamishina Bakori ya jaddada alakar da ke tsakanin safarar miyagun kwayoyi da aikata laifuka masu hadari, yana mai cewa kama mutanen da kwace kayayyakin sun nuna irin nasarar da ake samu wajen rage irin wadannan laifuka.

Ya bukaci al’umma da su ba da goyon baya ta hanyar bayar da sahihan bayanai domin tabbatar da zaman lafiya a Kano.