Wata Babbar Kotun Jihar Akwa Ibom da ke zamanta a birnin Uyo, ta bayar da umarnin kamawa tare da tsare wani mutum mai suna Henry Edet Unung saboda rashin sauke nauyin ’ya’yansa da rataya a wuyansa.
Mai Shari’a Ntong Ntong ne ya bai wa Kwamishinan ’Yan sandan jihar umarnin ɗaure mutumin na tsawon wata guda a Kurkukun Uyo saboda watsi da ɗawainiyar ’ya’yan da ya haifa.
- AFCON: Yadda Za Ku Kaucewa Bugun Zuciya Yayin Kallon Kwallo
- Ta’ammali da miyagun kwayoyi na haddasa ta’addanci a Borno — NDLEA
Aminiya ta ruwaito cewa, alƙali ya bayar da wannan umarnin ne yayin yanke hukunci kan ƙarar da matar mutumin uwar ’ya’ya uku ta gabatar a kotun.
Kotun ta ce Mista Unung ya yi mata rashin ɗa’a da gangan sakamakon bijire wa wani umarni da Mai Shari’a Iboro Ukapana ya bai wa wanda ake kara tun a shekarar 2018.
Mai Shari’a Ntong ya ce wanda ake karar ya yi biris da umarnin da aka ba shi tun a ranar 9 ga watan Nuwamban 2018, inda aka tilasta masa biyan N20,000 duk wata da kuma buhun shikafa da wake da garri da sauran kayayyakin abincin da ’ya’yansa za su ci.
“Kotu ta bayar da umarnin cewa wanda ake kara ya riƙa biyan Naira 20,000 duk wata a matsayin kuɗin dawainiya, da kuma sayen buhun shinkafa da wake, garri da sauran kayan abinci da biyan kuɗin makaranta, kula da lafiya da sutura da sauran larurorin ’ya’yansa.
“Wannan ya nuna cewa ka bijire wa umarnin Kotun, wanda babu shakka raini ne da rashin mutuntawa da cin mutuncin martabar Kotun,” inji alƙalin.
Alƙalin ya kuma ce a watan Satumbar 2019 ne Magatakardan Kotun ya aike wa wanda ake kara takardar tunatarwa da neman ya yi wa umarnin kotun biyayya amma ya bijire.
Mai Shari’a Ntong ya nanata cewa dole ne wanda ake karar ya ɗanɗana kuɗarsa saboda fusata kotun da ya yi wadda take da hurumin ɗaukar mataki kan duk wani wanda ya bijire mata.
“Haƙƙin Kotu ne ta hukunta duk wanda ya ƙi bin umarninta, sai dai za mu hukunta wanda ake ƙarar domin ya gane cewa bai kamata ya yi watsi da dawainiyar ’ya’yansa ba.
“Saboda haka yanzu muna bai wa ‘yan sanda su tsare wanda ake ƙarar a gidan yari na tsawon wata guda daga bisani kuma sai a sake gurfanar da shi a gaban Kotu domin ya wanke kansa daga wannan raini.
“Kamar yadda dokar kare haƙƙin yara ta Jihar Akwa Ibom ta tanadar, duk wani hukunci da aka yanke kan duk wata shari’a da ta shafi yara, ya kamata a fifita haƙƙin yara.”
Kotun ta kuma ɗage zamanta har zuwa ranar 28 ga watan Maris.