Kotun Musulunci a Jihar Kano ta tsare wasu mutum hudu a gidan yari kan zargin yin da shaye-shaye da kuma buga ludo a cikin wani masallaci.
Kotun Musulunci da ke unguwar PRP a Gama a Karamar Hukumar Nassarawa ta ba da umarnin ne bayan an gurfanar da mutanen wadanda duk mazauna unguwar Rimin Kebe ne.
- ’Yan bindiga sun kashe manoma 4 sun sace 8 a Katsina
- An tsare matashi kan tsokanar budurwa da ‘kin iya Kunu’ a Kano
Tun da farko wani Auwalu Usman ne ya yi karar cewa mutanen hudu sun hada baki suna shiga masallaci domin yin wasan ludo da kuma shaye-shaye.
Ya ce yayin da ya yi yunkurin hana su, sai suka taru suka yi masa dukan tsiya tare da yi masa barazana cewa ya yi musu katsa-landan a harkokinsu.
Wanda ake kara na farko ya amince da laifin da ake tuhumar sa, yayin da sauran ukun suka musanta zargin da ake yi musu a lokacin da mai gabatar da kara, Aliyu Abidin Murtala ya karanta musu tuhume-tuhumen.
Alkalin kotun, Malam Nura Yusuf Ahmed, ya bayar da umarnin ci gaba da tsare su a gidan gyaran hali har zuwa ranar 3 ga watan Janairun 2024, domin gabatar da shaidu a gaban kotu.