✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun kashe manoma 4 sun sace 8 a Katsina

’Yan bindiga sun kashe manoma hudu sun sace wasu takwas a kauyen Nahuta da ke Karamar Hukumar Batsari a Jihar Katsina.

’Yan bindiga sun kashe manoma hudu sun sace wasu takwas a kauyen Nahuta da ke Karamar Hukumar Batsari a Jihar Katsina.

Kakakin ’yan sandan jihar, ASP Abubakar Aliyu, ya ce a ranar Asabar manoman suna girbin amfanin gonakinsu ne maharan suka kai farmaki.

Daya daga cikin manoman da ya tsallake rijaya da baya da raunukan harbin bindiga, ya ce. “’yan fashin ne suka far wa manoman.

“Sun bude musu wuta suka kashe hudu suka raunata daya; sun kuma yi awon gaba da wasu takwas,’’ inji Aliyu.