Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke Abuja ta soke zaɓen ’yan Majalisar Dokokin Jihar Filato na jam’iyyar PDP su 11, sannan ta ayyana ’yan APC a matsayin halastattun waɗanda suka lashe kujerun.
A wani hukunci da suka yanke da murya ɗaya ranar Juma’a, alkalan da ke ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Okon Abang, sun ce duk kuri’un da dakatattun ’yan majalisar suka samu a zabensu na watan Maris lalatattu ne saboda jam’iyyarsu ba ta da shugabanci.
- Babu hannun Tinubu a shari’ar zaben Kano – Kungiyar Yarabawa
- Kotu ta soke zaben Kakakin Majalisar Dokokin Bauchi
Alkalin ya ce PDP ta yi wa tanade-tanaden sashe na 177 na kundin tsarin mulkin Najeriya kara tsaye, don haka ba ta cancanci ta tsayar da ’yan takara ba a zaɓen.
Daga nan ne kotun ta ayyana dukkan waɗanda suka zo na biyu a zaɓen a matsayin waɗanda suka lashe shi.
’Yan majalisar da aka dakatar dai sun haɗa da; Hon Timothy Dantong (Riyom), Hon. Rimyat Nanbol,- (Langtang ta Arewa ta Tsakiya), Moses Sule (Mikang), Salome Waklek, (Pankshin), Hon. Bala Fwangji (Mangu ta Kudu), Hon. Maren Ishaku (Bokkos), Hon. Dagogot (Quaanpan ta Arewa) da Nannim Langyi,-(Langtang ta Arewa).
Sauran sun haɗa da Nimchak Rims (Langtang ta Kudu) Hon. Danjuma Azi (Jos ta Arewa maso Yamma) Gwottson Fom (Jos ta Kudu) and Hon. Abubakar Sani Idris (Mangu ta Arewa).
Sakamakon wannan hukuncin dai, yanzu jam’iyyar ta APC ce ta koma mai rinjaye a majalisar Jihar.