✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta soke zaben Kakakin Majalisar Dokokin Bauchi

Kotun ta ce za a sake zabe a rumfuna 10 na mazabar Kakakin majalisar

Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke Abuja ta soke zaben kujerar Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Bauchi, Abubakar Yakubu Suleiman, daga matsayin dan majalisar wakiltar mazabar Ningi ta tsakiya.

Kotun, wacce ta yanke hukunci ranar Juma’a ta kuma bayar da umarnin sake zabe a rumfuna 10 da ke mazaɓar.

Hukumar Zabe ta Ƙasa (INEC) dai ta bayyana Abubakar na jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben da aka gudanar ranar 18 ga Maris, bayan ya sami kuri’u 16,866, inda ya kayar da babban abokin hamayyarsa, Khalid Abdulmalik Ningi na jam’iyyar APC wanda ya samu quri’u 15,065.

Sai dai Khalid bai gamsu da sakamakon ba, inda ya kalubalanci nasarar Abubakar a gaban kotun sauraron kararrakin zaben.

Amma kotun ta yi watsi da karar ta kuma tabbatar da nasarar Abubakar a karo na biyu.

Shi ma dan takarar na APC bai gamsu da hukuncin kotun ba, inda ya garzaya kotun daukaka kara ya qalubalanci hukuncin da kotun ta yanke.

Kuma a hukuncin da ta yanke a ranar Juma’a, aljalan kotun mai mutane uku , sun yi jingine hukuncin da kotun ta yanke tare da bayar da umarnin sake gudanar da zabe a rumfunan zabe 10.

Dangane da hukuncin, Kakakin majalisar, a wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai Abdul Burra ya aike wa manema labarai, ya bayyana hukuncin a matsayin wani karamin koma-baya wanda ba sabon abu ba ne a siyasa.

Sai dai ya ce duk da hukuncin bai yi masa dadi ba, ya yi kira ga magoya bayansa da su kwantar da hankalinsu.