Wata kotun majistare ta tsare wani limamin coci a gidan yari kan laifin yi wa wata matashiya mai shekaru 22 fyade.
Babbar Kotun Majistare da ke Badagry a Jihar Legas ta tisa keyar Fasto Sunday Adewoye zuwa gidan yarin ne a ranar Talaa bayan an gurfanar da shi.
Dan sanda mai gabatar da karar, Insfekta Ayodele Adeosun, ya shaida wa alkali cewa a ranar 17 ga Afrilu, 2024 ne Fasto Adewoye ya zakke wa matar da karfin tsiya a garin na Badagry.
Hakan a cewarsa laifi ne a karkashin dokar hukunta manyan laifuka ta Jihar Legas.
- Gwamnati ta yi wa ma’aikata da ’yan fansho karin albashi
- Masu kwacen waya sun caka wa budurwa wuka a Yobe
Mai shari’a Patrick Adekomaiya ya ba da umarnin tsarewar ne bayan da ya ki sauraron rokon fasto Adewoye, mai shekaru 45.
Daga nan kotun ta dage zaman zuwa ranar 3 ga watan Yuni domin samun shawara daga hukumar shari’a ta jihar.
(NAN).