Gwamnatin Tarayya ta kama mutum 347 da ake zargi da haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba a sassa daban-daban na Najeriya, inda aka gurfanar 143 a kotu.
Kama mutanen ya biyo bayan kafa wata runduna a shekarar 2024 don daƙile ayyukan haƙar ma’adanai ba ƙa’ida ba.
- Kotun ƙoli ta tabbatar da Anyanwu a matsayin sakataren PDP
- Kwankwaso ya yi Allah-wadai da ayyana dokar ta-ɓaci a Ribas
Ministan Ma’adanai, Dele Alake, ya ce gwamnati na ƙoƙarin tabbatar da an hukunta mutum 327 da ke gaban kotu.
“A wannan watan, Babbar Kotun Tarayya da ke Ilorin ta yanke wa wasu ‘yan kasashen waje guda biyu, Yang Chao da Wu Shan Chuan, hukuncin ɗaurin gidan yari kan haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba.
“Muna jinjina wa EFCC saboda ƙoƙarinta na gurfanar da masu aikata laifin,” in ji Alake.
Ministan ya ƙara da cewa runduna da aka kafa ta ƙwato wuraren haƙar ma’adanai guda 98, kuma ta gano wasu haramtattun wurare guda 457.
Gwamnati na shirin faɗaɗa ayyukan rundunar zuwa wasu jihohi tare da amfani da fasaha kamar jiragen sama marasa matuƙa da sauran na’urori don sanya ido.
“Rundunar ta ƙwace wuraren da wasu suka mamaye sama da shekaru 10 ba bisa doka ba.
“Wannan zai taimaka wajen bunƙasa kuɗaɗen shiga daga ɓangaren ma’adanai,” in ji shi.
Ministan ya tabbatar da cewa gwamnati za ta ƙara yawan jami’an tsaro da kayan aiki domin daƙile ayyukan haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba.
Ya gargaɗi duk masu aikata irin waɗannan laifuka da su daina, ko kuma su fuskanci hukunci.