✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama mutum 3 kan zargin sata da ƙone gidan bature a Gombe

Rundunar ta ce za ta gurfanar da su a gaban kotu da zarar ta kammala bincike.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe, ta kama wasu mutum uku da ake zargi da laifin sata da kuma ƙone gidan wani Bature a unguwar G.R.A, kusa da gidajen ’yan majalisa a jihar.

Waɗanda aka kama sun haɗa da Hannatu Ibrahim mai shekaru 28 daga Kumo, Ahmed Adamu mai shekaru 20, da Abubakar Ibrahim mai shekaru 28.

A cewar kakakin rundunar, DSP Buhari Abdullahi, lamarin ya faru ne ranar 22 ga watan Maris, 2025 da misalin ƙarfe 8 na dare.

Sanarwar ta bayyana cewa Hannatu Ibrahim, wacce ke aiki a matsayin mai girki ga Mohammed Jurdi, wanda ɗan kasar Siriya da ke aiki da kamfanin Triacta Nigeria Limited, ta sace dala 35,000 (kimanin Naira miliyan 53.5) tare da banka wa gidan wuta.

Bayan samun rahoton, ‘yan sanda sun garzaya wajen, inda suka kama ta tare da gano dala 7,100 a wajenta.

A yayin bincike, ta ce Ahmed Adamu ne, mutum na farko da ta tuntuɓa bayan aikata laifin.

An samu dala 100 a cikin sakar hannunsu.

An kuma kama Abubakar Ibrahim, mai gadin gidan da aka yi satar, wanda ake zargi da taimaka musu wajen aikata laifin.

DSP Abdullahi, ya ce suna ci gaba da bincike, kuma suna shirin gurfanar da waɗanda ake zargi a gaban kotu.

Ya kuma tabbatar wa jama’a cewa rundunar za ta ci gaba da yaƙi da laifuka tare da tabbatar da adalci a jihar.