✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta ci ’yan majalisar Filato da ta kora tarar N128m

Kotu ta ci tarar ’yan majalisar dokokin jihar Filato da aka kwace kujerunsu a watan Nuwamban 2023, kudi Naira miliyan 128.

Kotun daukaka kara ta ci ’yan Majalisar Dokokin Jihar Filato wadanda aka kwace kujerunsu a watan Nuwamban 2023 tarar kudi Naira miliyan 128.

An ci ’yan majalisar su 16 tarar Naira miliyan 8 kowannensu ne bayan kotun ta yi watsi da karar da suka shigar na neman a sake neman ta sake duba hukuncin da ta yanke a baya na korar su.

Amma alkalan kotun da ke zama a Abuja karkashin jagorancin JOK Oyewole sun yi watsi da karar da cewa ba ta da tushe balle makama.

’Yan majalisar da aka kora, sun sake garzayawa kotun suna neman a dawo da su kan kujerunsu a majalisar dokokin jihar ne bayan da kotun koli ta tabbatar da zaben Ggwamna Caleb Muftwang.

Amma bayan sauraron su, mai shari’a JOK Oyewole ya ki amincewa da kudirin saboda rashin cancanta, inda ya bayyana karar a matsayin bata lokacin shari’a.

Idan za a iya tunawa, kotun daukaka kara ta kori ’yan majalisar ne kasancewar jam’iyyarsu ba ta da shugabanci don haka ba za ta iya tsayar da ’yan takara a zabe ba.

A dalilin haka ne ta bayyana duk wadanda suka zo na biyu a zaben na 2023 a matsayin wadanda suka yi nasara.

Aminiya ta ruwaito cewa shugaban majalisar jihar, Gabriel Daweng, ya ki rantsar da yan jam’iyyar APC da na Labour 16 a matsayin ’yan majalisa a ranar 23 ga watan Janairu, inda ya ce ya samu umarnin kotu, inda ya bukaci su dakata har kotu ta yanke hukunci.