Wani jigon dan siyasa kuma Basaraken gargajiya a Jihar Gombe, Alhaji Ibrahim Haruna, ya bayyana cewa hana Mata kaso 35 cikin 100 na mukaman gwamnati ba hikima ba ce a siyasance.
A cewar Alhaji Haruna da ke zaman Sarkin Hausawan Takulma, ko a kasashen da suka ci gaba irin Amurka da Ingila wadanda suka assasa tsari na dimokuradiyya kuma muke koyi da su, Mata na da kaso mai tsoka a mukaman gwamnati.
- Babu wani aibu a sauya jam’iyya a siyasa —Kwankwaso
- Gwamnati ta haramta wa ’yan Najeriya tafiya Ukraine domin yakar Rasha
Alhaji Ibrahim Haruna, y ace a matsayinsa na dan siyasa kuma basaraken gargajiya da ya yi yawo a kasashen duniya bai ga inda Mata ke taka rawar gani a siyasa kuma ake barin su a baya ba sai Najeriya, domin kuwa su ne ke da mafi rinjayen kuri’u.
Ya ce “kamata ya yi yadda mata ke fitowa kwai da kwarkwata don yin zabe, su ma ya kamata a basu kaso daidai da mazaje amma sai gashi kashi 35 ma da suka nema wanda bai kai rabi ba an hana su.
“Idan haka ne mene ne amfanin fitowarsu su zabi namiji wanda ko iya su kadai suka marawa Mace baya za ta kai ga cin zabe amma ana ta kokarin take su a lokacin da ake kokarin ganin cewa sun fito sun shiga harkokin siyasa ana damawa da su.
“Kasashe irinsu Ingila da Amurka da Jamus da ake koyi da su a siyasa har shugabanin kasa Mata sun yi kuma sun taka rawar gani sosai fiye da wasu mazan, to idan haka ne kuwa me zai sa a Najeriya kashi 35 cikin 100 din ma ba za’a basu ba.
Ya ba da misali da wasu jihohi inda ya ce ko ’yan majalisun jiha Mata ba’a samu, “babu manyan sakatarori Mata, kuma yanzu haka a Gombe Mace da ya ce tilo ’yar majalisar Tsara Dokokin Jihar, ’yar Majalisar Wakilai ta Tarayya ma daya ce.
“Maimakon a basu tikiti na alfarma a duk mazabun dan majalisa mai kujeru biyu a bai wa Mace daya sannan Namijin kuma ya fafata da sauran ’yan takara.
Kazalila, Alhaji Haruna ya yi kira ga mahukuntan kasar nan da cewa su duba su gani hana Matan wannan dama zai haifar da matsala domin ana maganar kungiyoyin fararen hula guda 180 za su gudanar da zanga-zangar lumana a kofar shiga zauren Majalisar Tarayya da ke Abuja.
Ya ce “mene ne amfanin hakan wanda idan ba’a gyara ba su ma za su jagoranci irin wannan zanga-zangar amma za su yi ta ne a kan hana Mata fitowa su zabi duk wani namiji a kujerar siyasa.”