Mai Magana da Yawun Kungiyar Dattawan Arewa (NEF), Dokta Hakeem Baba-Ahmed, ya ce kashi 90 cikin 100 na gwamnonin Najeriya ba su cancanci ko da samun kusanci da shugabanci ba.
Dokta Hakeem Baba-Ahmed ya kara da cewa a cikin kowadanne gwamnoni 10 a Najeriya, mutum tara, “Ba su da shiri, ba su da kwarewa kuma ba su cancanci shugabanci ba.”
- Karin kudin mai zai jefa karin ’yan Najeriya cikin talauci —Abdulsalami
- An kama motoci cike da buhunan tabar wiwi a garin Kano
Ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi a Babban Taron Tattaunawa na Daily Trust na Shekara-shekara karo na 19 a Abuja, ranar Alhamis.
Baba-Ahmed ya ce a halin yanzu, mutanen da ba su dace ba ne suke jagorantar mutane suke musu karfa-karfa, su kuma mutanen suke ta neman samun sabbin shugabannin da suka dace, wanda shi ma bai wadatar ba.
Don haka ya yi kira da a sauya fasalin tsarin Najeriya, yana mai cewa, “Abin da ya kamata shi ne mu dora tsarin federaliyya da muke bi a kan gadon fida mu tambayi kanmu, ina matsalar take?
“Me ya hana a rage karfin shugabanci ko gudanar da shi, a sauya tsarin kasa, amma na san wannan batu ne da shugabannin yanzu suke yawan amfani da ita.”