✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Karin aure: Maza ku yi adalci, mata ku daina tsoro —Malamai

Malamai sun shawarci mata su daina jin tsoron idan mazajensu za su kara aure, suna masu kira ga magidanta su yi adalci a tsakanin iyalansu

Malaman Musulunci sun gargadi magidanta masu mata fiye da daya da su tabbatar da adalci a tsakaninsu domin kauce wa fushin Allah.

Sun kuma shawarci matan aure da su daina tsoron karin auren mazajensu, su kyautata zato.

Malaman sun yi wannan kira ne a yayin taron wa’azin da aka gudanar da taken, “Auren fiye da mace daya yadda Allah Ya hukunta,” wanda Kungiyar Al’ummar Lekki (LEMU) da je Jihar Legas ta shirya.

Babban Limamin Babban Masallacin Lekki, Dokta Ridwan Jamiu, ya bayyana wa mahalarta taron cewa mazajen da ba sa adalci a tsakanin matansu za su gamu da fushin Allah, don haka ya gargadi mazaje su guji auren mace fiye da daya saboda sha’awa ko rashin cikakken iliminsa.

Da yake jawabi kan dalilai da sharudan auren fiye da ce daya, malamin ya ce akwai gidaje da dama da mata fiye da daya inda ake zaman lafiya.

“Mun lura akwai mutane da dama da suka auri mace fiye da daya ba tare da ilimin lamarin ba, sun yi ne kawai saboda sha’awa. A karshe sai kare da zaluntar matan suna cutar da su siddan. Amma da sun san bala’in da zai same su a sakamakon hakan, da ba su fara ba.

“Annabi (SAW) ya ce duk mai mace fiye da daya da ya karkata ga wata da yi watsi da dayar, to a ranar Lahira za a tashe shi da barin jikinsa a shanye,” in ji malamin.

Amma ya kara da ewa auren mace fiye da daya abu ne da ba za a raba shi da al’ummar Nijeriya ba.

A nasa jawabinsa kan an kula da mace fiye da daya, Daraktan Cibiyar Daaru Sa’adah, Sheikh Abu Labeebah Taofeek Busari, ya jaddada muhimmanci nuna kulawa da tausaya wa juna da kuma fahimtar juna a tsanin ma’aurata.

A nata bangaren, malamar koyar da zamantakewar auren mace fiye da daya, Hajiya Maryam Nurudeen-Arole, ta bayyana cewa karin aure abu ne da Allah Ya hukunta a cikin littafinsa, don haka mata su kwana da shirin zuwansa.