Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta fara raba kayan zabe masu muhimmanci ga yankunan da za a sake gudanar da zaben a Jihar Adamawa a ranar Asabar.
INEC ta bayyana zaben gwamnan jihar da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris a matsayin wanda bai kammala ba, sakamakon adadin kuri’un da aka tattara da wadanda aka soke ya zarce tazarar da wanda ke gaba ya bai wa na biyu.
- ‘Yan sanda sun ceto mutum 9 da aka sace a Zamfara
- Hauwa: Bafulatanar daji da ta dauki nauyin karatun danta zuwa jami’a
Zaben dai an fafata ne tsakanin Sanata Aishatu Binani ta jam’iyyar APC da kuma gwamna mai ci, Umar Fintiri na jam’iyyar PDP wanda ke kan gaba da kuri’u sama da 30,000.
Kwamishinonin INEC guda biyu, Farfesa Abdullahi Abdulzuru da Dokta Baba Bola ne suka halarci wajen sanya ido kan yadda aka raba kayan zaben ga jami’an hukumar a wannan Juma’ar.
Da yake jawabi ga manema labarai, Kwamishinan Zabe a jihar, Barista Hudu Ari, ya ce hukumar ta shirya kuma za ta gudanar da sahihin zabe cikin lumana.
“An aike da duk kayan zabe. Za su isa inda ake bukata a kan lokaci, ”in ji shi.
Ya kuma bukaci magoya bayan jam’iyyu da su guji duk wani nau’in tashin hankali, su kasance masu bin doka da oda a lokacin zabe da kuma bayansa.
A halin da ake ciki, rundunar ‘yan sandan Jihar Adamawa tare da hadin gwiwar jami’an tsaro zaune cikin shirin ko-ta-kwana domin tunkarar duk wasu bata gari.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Suleiman Yahaya Nguroje, a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai, ya shawarci jama’a da su kai rahoton duk wani abu da gamsu da shi ba ga ‘yan sanda.