Harry Kane ya zama na biyu a jerin wadanda ke kan gaba a cin kwallaye a Firimiyar Ingila a tarihi.
Tottenham ta doke Crystal Palace 1-0 a wasan mako na 35 a Premier League ranar Asabar, kuma Harry Kane ne ya ci kwallon.
- An kawo karshen annobar COVID-19 —WHO
- Real Madrid za ta kece raini da Osasuna a wasan karshe na Copa del Rey
Kane, mai shekara 29, kenan zura na 209 a raga a babbar gasar tamaula ta Ingila, kenan ya zarce tsohon dan wasan Manchester United, Wayne Rooney.
Tsohon dan wasan Newcastle United Alan Shearer shi ne kan gaba mai 260 a raga, yayin da Wayne Ronney ya koma na uku mai 208 a Premier League.
Wannan ce nasarar farko da Tottenham ta samu karkashin kociyan rikon kwarya, Ryan Mason.
Tottenham ta koma ta shida a kan teburi da maki 57, sai dai ranar Litinin Brighton, wadda take ta bakwai da maki 55 za ta kece raini da Everton.
Ita kuwa Tottenham za ta je gidan Aston Villa ranar Asabar 13 ga watan Mayu.