✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tarihi 19 da aka gaza karyawa a gasar Premier

Ryan Giggs shi ne dan kwallon da ya fi cin kofi a tarihin gasar Premier.

Bayan da aka shiga mako na biyu kuma ake shirin shiga mako na uku da fara fafata gasar Premier ta Ingila, mun waiwaya baya don zakulo wasu daga cikin abubuwan tarihi da kungiyoyi da kuma ’yan kwallo suka kafa wadanda aka gaza karya su har zuwa kakar da ta gabata.

Shin ko bana za a karya wadannan abubuwan tarihi ko kuwa za su ci gaba da zama daram ba tare da an karya su ba.

Ga abin da muka kalato kamar haka:

1. Cristiano Ronaldo ya lashe dukkan kofunan da dan wasa tilo ke samu a shekarar 2008.

2. Erling Haaland ya jefa kwallo uku-uku rigis a cikin wasa takwas.

3. Liverpool ta hada maki 97 a gasar Premier amma ba ta lashe gasar wannan kaka ba.

4. Jamie Vardy ya zama dan wasa na farko da ya jefa kwallo a wasa 11 a jere, inda ya karya tarihin da Ruud van Nistelrooy ya kafa na jefa kwallo a wasa 10 a jere a shekarar 2015.

5. Petr Cech ya kafa tarihin golan da ya fi hana kwallon shiga ragarsa a gasar Premier (inda aka yi wasa 24 ba tare da jefa masa kwallo a raga ba) a kakar wasa ta shekarar 2004/2005.

6. Manchester City ta zama kungiyar da ke buga gasar Premier ta farko da ta hada maki 100 a kakar wasa ta shekarar 2017/2018.

7. Sadio Mane ya jefa kwallo uku mafiya sauri a tarihin gasar Premier, inda ya ci kwallo ukun a cikin minti biyu da dakika 56 a wasansu da Aston Villa a shekarar 2015.

8. Frank Lampard shi ne dan wasan tsakiya da ya fi jefa kwallo a raga a tarihin gasar Premier, inda ya ci kwallo 177.

9. John Terry shi ne mai tsaron baya da ya dukkan masu tsaron baya jefa kwallo a raga a tarihin gasar Premier inda ya ci kwallo 41.

10. Arsenal ta jagorancin teburin gasar Premier na sama da kwana 250 ba tare da ta lashe gasar ba.

11. Edwin Ban Der Sar ya kafa tarihin mafi jeranta tsare raga da buga wasa 14 ba a ci shi ba, kuma ya yi minti 1,311 ba tare da an jefa masa kwallo a raga ba, lokacin da ake buga wasa.

12. Jose Mourinho lokacin da yake horar da Chelsea ya kafa tarihin jefa wa kungiyarsa kwallo 15 a kakar wasa ta 2004/2005 ta gasar Premier.

13. Alan Shearer shi ne wanda ya fi kowa jefa kwallo a tarihin gasar Premier ta Ingila, inda ya jefa kwallo 260 a gasar.

14. Ryan Giggs shi ne dan kwallon da ya fi cin kofi a tarihin gasar Premier, inda ya lashe gasar sau 13.

15. Arsenal ta ci gaba da zama kungiyar da ta buga wasa ba tare da an samu nasara a kanta ba a gasar Premier a kaka guda a shekarar 2003/2004.

16. Chelsea ta kafa tarihin kungiyar da aka dauki lokaci mafi tsawo ba tare da an lallasa a gidanta ba, inda ta buga wasa 86 ba a ci ta a gida ba.

17. A kakar wasa ta 2021/2022 Chelsea ta kammala rabin kakar ba tare da wata kungiya ta samu nasara a kanta.

18. Leicester City ita ce ta kafa tarihin zama kungiya ta farko da ta fito daga ajin ’yan dagaji amma ta lashe gasar Premier a shekarar 2015/2026.

19. Manchester United ta kafa tarihin cewa matukar ta fara jefa kwallo a ragar abokiyar karawarta a wasanta na gida a farkon rabin lokaci, to ba za a samu nasara a kanta ba, tun daga 1984, inda tarihi ya nuna ta samu nasara a irin haka a wasa 263, ta yi kunnen doki 16, kuma ba a samu nasara a kanta ba.