Tsohon tauraron ƙungiyoyin Manchester United da Real Madrid, Ruud van Nistelrooy ya ajiye aikinsa na horas da Leicester City bisa fahimtar juna.
Wannan na zuwa ne bayan da a ƙarƙashin jagorancinsa ƙungiyar ta yi wasanni 27 da ta gaza taɓuka abin a zo a gani a cikinsu, lamarin da ya kai ta ga faɗawa gasa mai daraja ta biyu a Ingila wato Championship.
Wata sanarwa da kungiyar ta fitar, ta ce an cimma matsaya tsakaninta da Van Nistelroy ne bayan tattaunawar da suka yi.
A ƙarshen watan Nuwamban da ya gabata, bayan da ta kori Steve Cooper a lokacin da suke matsayi na 16 a gasar Firimiyar bara, Liecester City ta ƙulla yarjejeniya da Van Nistelrooy, kwangilar da ba za ta ƙare ba sai a shekarar 2027.
To amma duk da sauyin da aka samu kwalliya ta gaza biyan kuɗin sabulu domin kuwa a haka suka yi ta tafiya da ƙyar.
Daga ƙarshe ma dai ƙungiyar ta sha kashi da ci 1-0 a karawar ta Liverpool a ranar 20 ga watan Afrilu, rashin nasarar da ta tabbatar da cewar ƙungiyar ta yi adabo da gasar Firimiya sai kuma wani jiƙon.
A halin yanzu dai ana sa ran tsohon Kocin Burnley da Everton, Sean Dyche ya maye gurbin da Nistelrooy ya bari.