✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Van Nistelrooy da Lampard sun samu aikin horaswa a Ingila

Leicester City ta naɗa Ruud van Nistelrooy a matsayin sabon kocin ƙungiyar. Van Nistelrooy ɗan asalin Netherland zai maye gurbin Steve Cooper, wanda aka kora…

Leicester City ta naɗa Ruud van Nistelrooy a matsayin sabon kocin ƙungiyar.

Van Nistelrooy ɗan asalin Netherland zai maye gurbin Steve Cooper, wanda aka kora a makon da ya gabata bayan jan ragamar ƙungiyar a wasanni 12 na gasar Firimiya ta bana.

Ya sanya hannu kan yarjejeniyar shekara uku wadda za ta kai har watan Yunin 2027.

Naɗin Nistelrooy na zuwa ne makonni biyu bayan da ya bar muƙaminsa na kocin riƙon ƙungiyar Manchester United.

Coventry ta ɗauki Lampard

Kazalika, an naɗa tsohon ɗan wasan tsakiya na ƙungiyar ƙwallon ƙafar Chelsea da ƙasar Ingila, Frank Lampard ya zamo kociyan Coventry a bisa yarjejeniyar shekaru 2 da rabi.

Lampard ya maye gurbin Mark Robins, wanda aka sallama a farkon wannan watan.

A halin yanzu Coventry na mataki na 17 a gasar zakarun bayan wasanni 17 inda suka yi rashin nasara a wasanninsu 4 na ƙarshe.

A matsayinsa na ɗan wasa, Lampard ya ci wa Chelsea kwallaye 211 a dukkanin gasar da ta buga a shekaru 13 da ya shafe a cikinta masu cike da daukar kofi.

Ya taɓa horas da ƙungiyoyin Chelsea da Everton a gasar Firimiya, haka kuma ya horas da ƙungiyar Derby County.

Lampard zai karɓi ragamar horas da Coventry a karon farko ranar Asabar mai zuwa inda za ta kara da ƙungiyar Cardiff City a filin wasa na Coventry Building Society.