✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kawo karshen annobar COVID-19 —WHO

COVID-19 ta kashe sama da mutane miliyan 20 a fadin duniya.

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ce an kawo karshen annobar COVID-19, wadda ta yi sanadin mutuwar mutane da dama tare da wargaza tattalin arziki da sha’anin zamantakewar duniya.

Wannan na zuwa ne bayan sama da shekaru 3 da WHO ta ayyana cutar a matsayin annoba.

Shugaban hukumar Tedros Adhanom Ghebreyesus ne ya sanar da haka a jiya Juma’a, inda ya yi gargadin cewa har yanzu cutar na nan a matsayin barazana.

Wannan mataki na hukumar Lafiyar na zuwa ne bayan da kwamitin kwararru mai zaman kansa da ta nada a game da wannan cuta ta COVID-19 ya ce cutar ba a bukatar mayar da hankali sosai a kan cutar daga hukumar.

Sai dai a cewar Tedros, hatsarin cutar bai kau ba, inda ya yi kiyasin cewa ta kashe sama da mutane miliyan 20 a fadin duniya, kimanin ninki 3 na mutane kusan miliyan 7 da aka ce ta kashe a hukumance.

A ranar 30 ga watan Janairun shekarar 2020 ce hukumar Lafiya ta Duniya ta ayyana cutar COVID-19 a matsayin annoba, makwanni bayan da ta bulla a birnin Wuhan na kasar China.