✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda aka yi bikin nadin Sarkin Ingila Charles III

Wannan biki shi ne irinsa na farko tun bayan wanda aka yi a shekarar 1937.

Shugabannin Kasashen duniya da Sarakuna da kuma fitattun mutane sama da 2,300 suka halarci bikin nada Sarki Charles na III a matsayin wanda ya maye gurbin marigayiya Elizabeth ta biyu wadda ta rasu watanni 8 da suka gabata.

An gudanar da gagarumin bikin nadin Sarki Charles na III a wannan Asabar, inda Arcbishop na Canterbury ya sanya masa kambin sarautar Ingila, bikin da shi ne irinsa na farko cikin shekaru 70.

Wannan biki shi ne irinsa na farko tun bayan wanda aka yi a shekarar 1937 lokacin da aka nada mahaifiyarsa.

Da misalin karfe 12 na rana shugaban mabiya darikar Anglican, Archbishop Justin Welby ya dora hular zinare wadda ke zama hular mulki akan Sarki Charles a bikin da shi ne irinsa na farko tun bayan wanda aka yi a shekarar 1953.

Nan da nan taron mutane 2,300 da suka halarci bikin su ka kaure da sowa inda suke fadin ‘God Save the King’, ‘Allah Ya kare Sarki’ a gangamin da akayi a fadar Westminster Abbey, yayin da karar algaita ya mamaye wurin bayan kammala adu’o’in da aka yi na nadin sarautar.

A wajen dakin taron kuwa, an yi ta harba bindigogi ne a fadin kasar da kuma akan teku, tare da kada kararrawa a mujami’un da ke birnin Landan.

Bisa al’ada, Sarki Charles mai shekaru 74 sau guda zai sanya hular sarautar St Edward a lokacin mulkinsa, yayin da aka nada uwargidansa Camilla mai shekaru 75 a matsayin mai rike da mukamin sarauniya a wani kwarya kwaryar bikin da aka yi.

Kafin gudanar da bikin dai jami’an ‘yan sandan birnin London sun kama tarin masu zanga zanga wadanda ke adawa da masarautar da kuma korafi akan irin makudan kudaden da ake kashe mata.

Wasu daga cikin masu zanga zangar sun baje rubuce rubucen dake bayyana cewar, ‘wannan ba Sarkinmu bane’.

Kungiyar kare hakkin Bil Adama ta Human Rights Watch tare da Amnesty International sun bayyana damuwa akan yadda jami’an tsaro suka yi ta kama masu adawa da bikin, yayin da HRW ta ce a birnin Moscow kawai ya dace aga irin wannan kame, amma ba Ladan ba.

Rundunar ‘yan sandan Landan ta baza jami’anta 11,500 a titunan birnin domin tabbatar da tsaro, yayin da ta gargadi duk masu shirya zanga zanga.

Barakar Masarautar Ingila ta fito fili

Yayin gudanar da bikin nadin, matsalar da ke tsakanin ’ya’yan gidan sarautar ta sake fitowa fili, ganin yadda aka zaunar da Yarima Harry da Andrew a layi na 3 na ’ya’yan gidan Sarautar, maimakon layin farko.

Yarima Harry wanda shi ne da na biyu na sabon Sarkin, sun janye daga ayyukan da suka shafi gidan sarautar tare da uwargidansa Meghan a shekarar 2020, yayin da suka dinga caccakar mutanen gidan sarautar akan yadda suka dinga nuna musu bambanci.

Yarima Harry da Andrew a layi na uku.

Shi kuwa Yarima Andrew wanda wa ne ga sabon Sarkin, ya gamu da fushin fadar ne saboda alakarsa da wani attajirin Amurka, Jeffrey Epstein da kuma zargin cin zarafin mata wanda aka sasanta ba tare da zuwa kotu ba.

Mahalarta bikin sun yi wa Yarima Andrew ihu lokacin da ya isa Westminster Abbey daga fadar Buckingham tare da sauran ’ya’yan gidan sarautar.

Wannan ne karo na farko da Yarima Harry ya shiga cikin tawagar ’ya’yan gidan sarautar tun bayan tonon sililin da ya musu a hirar da aka yada ta kafar talabijin.

Uwargidansa Meghan ta ki zuwa bikin da aka yi a Landan inda ta zauna gida a Amurka tare da ’ya’yan ta.