✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wata mata ta zama dodo bayan zanen tattoo a fuskarta

Ta yi iƙirarin an tilasta mata ta ɓuya cikin ciyayi lokacin da ta kai ’ya’yanta bakwai yawon shaƙatawa don kada ta tsoratar da kowa.

Wata mata mai suna Melissa Sloan ta ɓoye kanta daga bikin ala’ada da ake yi a gundumar Worcestershire da ke yankin West Midlands a Ingila lokacin da ta fitar da ’ya’yanta wurin bikin saboda maƙwabtanta suna tsorata sosai don ganin zanen tattoo da ta yi a fuskarta.

A yayin da bikin Halloween ke gabatowa, wanda ake yi a ƙarshen Oktoba a wasu ƙasashe, Melissa ta bayyana cewa, ba ta buƙatar sauya kamanninta ko yin ado don sauya fuskarta kamar dodo saboda yawan zanen tattoo da ta yi mai tsoratarwa.

Melissa Sloan ta yi zanen tattoo fiye da 800 a jikinta har zuwa fuskarta. Hak kuma a yayin da take son zanen jikinta, ta yarda cewa sau da yawa zanen yana haifar da matsala a rayuwarta ta yau da kullun ciki har da lokacin bukukuwan adon al’adu na sauya kamanni.

Melissa mai shekara 47 daga Kidderminster, Worcestershire, ta yi iƙirarin an tilasta mata ta ɓuya cikin ciyayi lokacin da ta kai ’ya’yanta bakwai yawon shaƙatawa don kada ta tsoratar da kowa.

A gidanta ma ba kasafai take samun baƙi ba, saboda yara suna tsoron kamanninta. “Ba na buƙatar kayan ado na bikin Halloween – zanen tattoona suna tsorata yara. Kamar da nake bayyana da ita a kullum tana tsoratar da su, amma dole ne in yi taka-tsantsan a lokacin da ake tashe-tashen hankula,” in ji ta

Melissa ta bayyana wa kafar yaɗa labarai ta What’s The Jam cewa: “Kamannina kullum suna tsoratar da su, amma dole ne in yi taka-tsantsan nan da lokacin kaɗan za a yi bikin. Ina jin baƙin cikin cewa ba zan ji daɗin Halloween sosai tare da ’ya’yana ba.

“Ba zan iya yin shiga cikin dabara ko sauyi mai kyau ba. Misali, yawancin maƙwabtana suna tsoron hulɗa da ni idan na fita gida da yarana. Don haka dole in ɓuya a cikin ciyayi.”

Ta bayyana cewa: “Idan na tafi tare da ’ya’yana, mutane suna firgita a lokacin da suka kale ni – kallon su yana gajiyar da ni. Amma a gidana, lokacin da na buɗe ƙafa don ba da kyautar alawa, wasu lokuta yara suna gudu. Wasu kuma su karɓa. Wasu ba su damu ba, sukan zo wurina.”

A wurin Melissa ɓoye fuskarta ba baƙon abu ba ne, dole ce duk da haka an dakatar da ita zuwa wurare da yawa saboda kamanninta kuma ta ƙaurace wa wurin cin abinci saboda mutane za su gudu.

Al’amarin ya ƙara ta’azzara, har ta kai ga yin kwalliya idan za ta fita waje, ta rufe zanen tattoo. Melissa ta ƙara da cewa, “abin kunya ce a ce mutane ba za su iya fahimtar fasahar fuskata ba.

“An tilasta ni in ɓuya, in ɓoye ainihin kamannina . Ya kamata mutane su yarda cewa, zanen tattoo nau’i ne na nuna kai. Har yanzu ni ce Melissa. Ina kawai nuna fasahata ce a kan fata ta don yaɗa adona a duniya, maimakon na rufe zanen.