Wani rahoto da hukumomin ƙasar Birtaniya suka fitar ya nuna Muhammad shi ne sunan da aka fi sanya wa jarirai maza a yankunan Ingila da Wales.
Alƙaluman da Ofishin Ƙididdiga na Ƙasar Birtaniya ya fitar ranar Alhamis ya nuna al’ummar yankunan Ingila da Wales da ke ƙasar sun fi raɗa wa ’ya’yansu maza suna Muhammad a kan kowane suna a shekarar 2023.
A ɗaya hannun kuma, rahoton ya nuna cewa farin jinin sunayen ’yan gidan Sarautar ƙasar na ƙara disashewa, inda ake samun ƙarancin jariran da ke zama takwara ga sunaye irin su Sarki Charles da George da Yarima Harrymda sauransu.
Rahoton, wanda Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters ya fitar ya ƙara da cewa yanzu sunan Muhammad ne kan gaba a tsakanin jarirai maza a Ingila da Wales, inda ya zarce sunan Noah (Nuhu) wanda a baya aka fi raɗawa a yankin.
Alƙaluman hukumomin Birtaniya sun nuna tun shekarar 2016 sunan Muhammad ya shiga cikin jerin sunaye 10 da ka fi raɗa wa yara sabbin haihuwa.
A shekara ta 2022 ya zama ba biyu wajen yawan waɗanda ake radawa, kamar yada Ofishin Babban Ƙididdiga na Ƙasar Birtaniya ya fitar.
Suna na uku da aka fi raɗa wa yara maza a yankunan a halin yanzu shi ne Oliver, wand ya maye gurbin George.
A ɓangaren mata kuma, sunan da aka fi sanya wa jarirai a 2023 shi ne Olivia sai Amelia da Isla.
Ofishin ya ƙara da cewa wasu sunayen da ke ƙara samun shahara a tsakanin jarirai a ƙasar su ne sunayen taurari kamar Reign da Saint daga iyalan Kardashian-Jenner sai kuma sunayen fitattun mawaƙa irin su Billie Eilish.