✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An ciro gawarwaki sama da 200 daga jirgin Indiya da ya yi hatsari

Shugaban hukumar kula da sufurin jiragen sama na Indiya ya ce jirgin na ɗauke ne da mutum 242, kuma akasarinsu Indiyawa ne.

Babban baturen ’yan sanda na birnin Ahmedabad da ke ƙasar Indiya ya bayyana cewa, an ciro gawar mutane sama da 200 na fasinjojin jirgin Air India da ya yi hatsari a yau Alhamis.

Babban jami’in ɗan sandan ya bayyana hakan ne a matsayin bayani na baya-bayan nan kan hatsarin jirgin, wanda ya rikito ƙasa jim kadan bayan tashi, kan hanyarsa ta zuwa birnin London na Birtaniya.

Shugaban hukumar kula da sufurin jiragen sama na Indiya ya ce jirgin na ɗauke ne da mutum 242, kuma akasarinsu Indiyawa ne.

Fasinjojin jirgin Indiya da yawa sun mutu a hatsarin

A cewar Kamfanin Dillancin Labarai na AP ya ambato shugaban ƴan sanda na birnin Ahmedabad na cewa akwai yiwuwar babu wanda ya tsira da ransa a hatsarin da jirgin sama mallakin kamfanin sufuri na India Air ya faru yau a birnin.

Ya bayyana hakan ne yayin da yake bayani kan hatsarin jirgin da ke kan hanyarsa ta zuwa birnin London na ƙasar Birtaniya.