✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum ɗaya ya tsira da ransa cikin 242 a hatsarin jirgin India

Kamfanin jirgin Air India ya ce, akwai fasinjojin Indiya 169 da 53 'yan Burtaniya da 'yan Portugal bakwai, da kuma wani ɗan ƙasar Kanada a…

Jirgin saman fasinja da ke kan hanyarsa ta zuwa Landan wanda ya yi hatsari a birnin Ahmedabad na Indiya a ranar Alhamis.

Mutum ɗaya ne ya tsira daga cikin mutane 242 da ke cikin jirgin, tare da fasa gine-ginen likitoci da iyalansu.

Wani ɗan jarida na AFP ya ga gawarwakin da aka zaƙulo daga wurin da jirgin ya faɗi, da kuma bayan jirgin ƙirar Boeing 787-8 Dreamliner a rataye a gefen wani gini da ya rutsa da shi a lokacin cin abinci.

“Iftila’in da ya afku a Ahmedabad ya ba mu mamaki da kuma ɓacin rai. Abin takaici ne da ba za a iya cewa komai ba,” in ji Firayim Minista Narendra Modi a bayaninsa bayan jirgin Air India mai lamba 171 ya yi hatsari bayan tashinsa.

Kwamishinan ’yan sandan birnin GS Malik ya ce gawarwakin fasinjoji da waɗanda abin ya rutsa da su a ƙasa na daga cikin 204 da aka gano zuwa yanzu, yayin da ma’aikatan lafiya ke jinya da dama waɗanda suka jikkata a birnin.

Yayin da aka fara fargabar mutuwar duk wanda ke cikin jirgin, jami’in kula da lafiya na jihar Dhananjay Dwivedi ya shaida wa AFP cewa “an tabbatar da wanda ya tsira” kuma ana jinyar shi a asibiti.

Ɗan jaridar na AFP ya ga wani gini ya ƙone ƙurmus bayan faɗuwar jirgin, inda hayaƙi ya turnuke sama da wani ɓangare na jirgin a ƙasa.

“Rabin jirgin ya faɗo cikin ginin mazaunin da likitoci ke zaune tare da iyalansu,” in ji Krishna, wani likita da bai bayyana cikakken sunansa ba.

Krishna ya ce ya ga “kusan gawarwaki 15 zuwa 20 da suka ƙone”, yayin da shi da abokan aikinsa suka ceto ɗalibai kusan 15.

Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Indiya ta ce, akwai mutane 242 a cikin jirgin, ciki har da matuƙan jirgi biyu da ma’aikatan cikin jirgin 10.

Kamfanin jirgin Air India ya ce, akwai fasinjojin Indiya 169 da 53 ‘yan Burtaniya da ‘yan Portugal bakwai, da kuma wani ɗan ƙasar Kanada a cikin jirgin da zai nufi filin jirgin saman Gatwick na Landan.