Wani ɗan siyasa da ya shahara mai suna K. Padmarajan, wanda ake yi wa laƙabi da “Sarkin Tsayawa Zaɓe” ya zama “Ɗan takarar da ake tsammanin ya fi kowa shan kaye a zaɓuka a duniya”.
Mutumin wanda ya yi takarar zaɓe sau 238 kuma yana shan kaye ya ce bai fitar da rai ba yana fatar samun nasara.
Padmarajan ya kasance dan siyasa mai juriya.
Ɗan siyasar mai shekara 65 daga Jihar Tamil Nadu a Indiya, mai gyaran motoci da injuna, ya shiga daruruwan zaɓuɓɓuka a cikin shekara 30 da suka gabata kuma ya kashe dubban dalolin Amurka kan yin rajistar takara.
Mafi kusancin takarar da ya taɓa samun nasara a zaɓe shi ne a shekarar 2011 lokacin da ya tsaya takarar Majalisar Wakilai a garin Mettur kuma ya samu ƙuri’a 6,273, inda ya zo na biyu a bayan wanda ya yi nasara – wanda ya samu ƙuri’a sama da 75,000 – kuma hakan ya sa shi fata cewa wata rana zai iya yin nasara.
Har yanzu wannan ranar ba ta zo ba, amma Padmarajan kwanan nan ya nuna cewa nasara ita ce burinsa na biyu.
Juriya da yarda da shan kaye su ne mabudin nasara kuma babu wanda ya fi shi.
“Dukkan ’yan takara suna neman nasara a zaɓuɓɓukan, ban yi ba,” in ji dan takarar.
Kuma ya ce ba da wasa yake ba. Bayan faduwarsa a zaɓe 238.
K. Padmarajan na neman tsawaita lokacin shan kaye ne kawai.
A bana zai yi takarar ta 239, kuma a wannan karo yana neman kujerar dan majalisa a Gundumar Dharmapuri ta Tamil Nadu.
Mai yiwuwa ba zai yi nasara ba, amma cin nasara ba komai ba ne.
Labarin Padmarajan ya fara ne a 1998 lokacin da ya yi takarar ƙaramar hukuma a garinsu ta Mettur.
Ya san kusan ba ya da wata dama, amma yana so ya nuna cewa kowane talaka yana da ’yancin tsayawa takara a hukumance.
A cikin shekara 30 da suka wuce, Sarkin Tsayawa Zaɓe ya sha kaye a zaɓuɓɓuka bayan yin takara da fitattun mutane kamar Firayi Ministan Indiya Narendra Modi ko magabatansa Atal Bihari Ɓajpayee da Manmohan Singh.
Amma yana sanya asararsa a kan hannun riga kuma yana da burin zama abin koyi ga matasa masu tasowa.
Don ƙarfafa wa mutane su bi sawunsa kuma su nuna juriya a rayuwarsu ta yau da kullun, K. Padmarajan, yana yawan tattaunawa da dalibai game da juriya da cin nasara.