Kungiyar Tarayyar Afirka (AU) ta zama sabuwar mamba a kungiyar kasashen G-20 masu karfin tattalin arziki ranar Asabar bayan Firaiministan India Narendra Modi ya gayyace ta.
Fadada kungiyar babbar nasara ce ta fannin diflomasiyya ga Modi, wanda zai sake fafatawa a zaben kasar a shekara mai zuwa kuma ya yi amfani da damar karbar bakuncin taron wajen kara wa kansa kima a idanun duniya.
- Gwamnati za ta gina gidaje 1,000 a jihohin Arewa 7 — Shettima
- Putin da Xi Jinping sun ƙaurace wa taron G-20
Kafin ya bude taron, Modi ya gaishe da shugaban Tarayyar Afirka kuma shugaban kasar Comoros Azali Assoumani inda ya rungume shi.
“India ta nemi a bai wa Tarayyar Afirka gurbi na dindindin na zama mamba a kungiyar G-20.
“Na yi amannar cewa kowa ya amince da hakan,” a cewar Modi a jawabinsa ga mahalarta taron.
“Ina kira ga shugaban Tarayyar Afirka ya zo ya zauna a kujerarsa ta dindindin a G-20 bayan amincewar kowa da kowa,” in ji shi, inda ya doka sandar da ke hannunsa wacce ke nuna an yarda da matakin.
Daga nan ne Assoumani ya je ya zauna a wurin da shugabannin kungiyar suka zauna bayan Ministan Harkokin Wajen, India S. Jaishankar ya yi masa iso.