✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Birtaniya za ta rage shekarun masu zaɓe zuwa 16

Ƙananan ƙasashe ne kawai ke ba wa yara masu shekaru 16 damar kaɗa ƙuri'a a zaɓen ƙasa, bisa ga bayanan shafukan intanet.

A ranar Alhamis  Gwamnatin Birtaniya ta bayyana cewa tana shirin bai wa yara ’yan shekaru 16 da 17 damar kaɗa ƙuri’a a babban zaɓen ƙasar, wani gagarumin sauyi da ya bai wa Birtaniyar damar zama mafi ƙarancin shekaru a faɗin duniya.

Hakan dai ya biyo bayan alƙawarin da Jam’iyyar Labour Party mai mulki ta yi na yin wannan sauyi gabanin samun nasara a zaɓen da ya gabata, kuma yana cikin wasu sauye-sauyen da ake shirin yi a tsarin dimokuraɗiyya.

Wasu dai na ganin hakan yana cikin ƙalubale saboda ƙarancin fitowar jama’a da dai sauransu.

Mai yiyuwa ne sauyin shekarun zaɓen zai iya haifar da cece-kuce, inda a baya masu suka suka yi ƙorafin cewa, yin hakan son kai ne saboda ana ganin sabbin matasan da ke da hannun jari za su iya goyon bayan Jam’iyyar Labour mai ra’ayin riƙau.

Firayim Minista Keir Starmer ya ce, “Ina ganin yana da matuƙar mahimmanci cewa ’yan shekaru 16 da 17 su sami damar kaɗa ƙuri’a, saboda sun isa fita aiki, sun isa biyan haraji, don haka (suna) biya.”

“Kuma ina ganin idan kuna biyan harajin, ya kamata ku sami damar faɗin abin da kuke son a kashe kuɗaɗen ku, ta wacce hanya ya kamata gwamnati ta bi,” in ji Starmer.

Dole ne gwamnati ta gabatar da doka a gaban majalisar dokoki, inda take da rinjaye, don yin sauye-sauye.

Ƙananan ƙasashe ne kawai ke ba wa yara masu shekaru 16 damar kaɗa ƙuri’a a zaɓen ƙasa, bisa ga bayanan shafukan intanet.

Sun haɗa da Ostiriya – ƙasa ta farko ta Tarayyar Turai  EU da ta rage shekarun jefa ƙuri’a zuwa 16 lokacin da ta yi sauyi a 2007 – da kuma Argentina da Brazil da Ecuador da Cuba.

Ministocin Kwadago a Birtaniya sun nace cewa, an yi wannan canjin ne don “sabunta dimokuradiyyar zamani ” da kuma ƙara yawan fitowar jama’a, tare da daidaita zaɓukan gama gari da shekarun da ake da su na kaɗa ƙuri’a na zaɓen ‘yan majalisun yankunan Scotland da Wales.