✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sifaniya ta lashe Gasar Euro ta 2024

Ingila ta shafe shekara 58 ba tare da ta lashe kofi ba.

Ƙasar Sifaniya ta lashe gasar Nahiyar Turai (Euro) ta 2024, bayan doke Ingila da ci 2 da 1 a filin wasa na Berlin da ke ƙasar Jamus.

Ɗan wasan gaban Sifaniya, Nico Williams ne ya fara jefa ƙwallo a minti na 47 bayan dawowa daga hutun rabin lokaci.

A minti na 73, ɗan wasan tsakiyar Ingila Cole Palmer ya warware ƙwallon da aka zura musu.

Ana gab da tashi daga wasan, Mikel Oyarzabal ya sake jefa wa Sifaniya ƙwallo ta biyu a raga.

Sifaniya dai ta lashe gasar Euro har sau kenan a tarihinta.

Kafin zuwa matakin wasan ƙarshe Sifaniya ta doke ƙasae Faransa da ci 2 da 1.

Ingila dai ta ƙare a mataki na biyu, wanda hakan ke nufin ta share shekara 58 ba tare da ta lashe kofi ba.