✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hana Biza: Najeriya ta cancanci a girmama ta – Babban Hafsan Tsaro

Ya jaddada cewar Najeriya ba za ta lamunci rashin girmamawa daga kowace ƙasa ba.

Babban Hafsan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa, ya gargaɗi ƙasashe cewa Najeriya ba za ta yarda da rashin girmamawa daga kowace ƙasa ba.

Ya bayyana hakan ne bayan da Ƙasar Kanada ta hana wasu jami’an sojin Najeriya takardae izinin shiga ƙasar, duk da cewa an gayyace su don halartar wasannin Invictus a Vancouver.

Da yake jawabi a Hedikwatar Tsaro da ke Abuja, bayan tarbar sojojin da suka halarci gasar, Musa ya nuna takaicinsa kan yadda ake nuna wa ‘yan Najeriya rashin adalci a wasu ƙasashe.

“Mun bi dukkanin matakan da suka dace. An aiko mana da gayyata, jami’an gwamnati sun sani, kuma mun cika dukkanin sharuɗa.

“Amma, ba san dalilin da ya sa aka hana jagororin tawagarmu kamar kaftin, likitan tawaga da mai duba biza. A. Tambayar ita ce, me ya sa?” in ji shi.

Musa ya jinjina wa sojojin da suka wakilci Najeriya a gasar, inda ya tabbatar musu da cewa gwamnati ba za ta bari su wulaƙanta ba.

“Sojojinmu da suka rasa wasu sassa jikinsu ko suka samu raunuka ba za a bari a wulakanta su ba.

“Za mu ci gaba da tallafa musu domin sadaukarwarsu ba za ta tafi a banza ba,” in ji shi.

Ya jaddada cewa Najeriya ta cancanci girmamawa, kuma ba za ta yarda da rashin adalci daga kowace ƙasa ba.