Ƙasar Saudiyya ta musanta batun da ake yaɗawa cewa ta sanya Najeriya a jerin ƙasashen da ta hana biza.
Sanarwar da aka yaɗa a kafofin sadarwa ta bayyana cewa daga ranar 13 ga Afrilu, Saudiyan za ta daina bai wa ƙasashen Masar, India, Pakistan, Morocco, Tunisa, Yemen da Aljeria bizar aiki, ta ziyara, da ta yawon buɗe idanu.
- Lakurawa sun kashe ’yan sa-kai 13 a Kebbi
- HOTUNA: Zanga-zangar adawa da gwamnatin Tinubu ta ɓarke a Abuja da Legas
“Rashin yin biyayya ga wannan tsarin ka iya jawo haramta shiga kasar sawon shekaru biyar” a cewar sanarwar.
Sai dai Cibiyar yawon buɗe ido ta Saudiyya ta bayyana wa manema labarai cewa waɗannan sabbin dokokin sun takaita ne ga lokacin aikin hajji.
“Duk wanda ke da bizar ziyara, ba zai yi aikin Hajji ko zama a birnin Makka ba tun daga ranar 10 har zuwa 14 ga Thul Qida. Bizar aikin Hajji za ta yi aiki ne kawai daga lokacin Hajjin.”