Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Real Madrid ta sake kafa sabon tarihi bayan doke ƙungiyar Pachuca, tare da lashe kofin Intercontinental.
Real Madrid ta fara jefa ƙwallonta ta farko ne, ta hannun ɗan wasanta, Kylian Mbappe a minti na 37 da fara wasa, bayan da Vinicius Junior ta taimaka masa.
- Za a saki matashin da aka yanke wa hukuncin kisa kan satar kaji a Osun
- Majalisar Dokokin Kano Ta Tabbatar Da Sabbin Kwamishinoni 7
Bayan dawowa daga hutun rabin lokaci, Rodrygo ya jefa ƙwallo ta biyu a ragar Pachuca a minti na 53, bayan samun taimako daga Mbappe.
Vinicius Junior, ya ƙarƙare da ƙwallo ta uku a minti na 84, a bugun fenareti.
Yanzu haka Real Madrid, ta lashe kofin Intercontinental karo na tara a tarihinta.
Har ila yau, a ranar Talata ne Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Duniya (FIFA), ta ayyana Vinicius Junior a matsayin gwarzon ɗan wasa na duniya na 2024.
Wannan na zuwa ne bayan ɗan wasan gaban na Real Madrid bai lashe kyautar Ballon d’Or ba.